Hajiya Asma’u Goro Ta Yi Rabon Tallafi Ga Mata Marasa Ƙarfi A Fagge.

Page Visited: 1703
0 1
Read Time:1 Minute, 28 Second

Daga Sadeeq Muhammad Fagge

Hajiya Asma’u Aminu Goro ta yi rabon tallafin jari da kayan gini ga mata da marayu a ƙaramar hukumar Fagge da ke jihar Kano.

Tun da fari matemaki na musamman ga Kwamared Aminu sulaiman Goro, Honorable Sabi’u ibrahim Banki, ya ce rabon tallafin ya biyo bayan koke da suka samu daga iyaye mata ne yasa ya bullo da wannan tallafi ta hannun matarsa. domin rage musu wahalhalu,

Ya kuma ƙara da cewa duba da irin ƙoƙarin da mata suke dashi musamman wajen baiwa yara tarbiyya da yadda suke rike gida yasa yake ƙoƙari wajen ganin suma sun samu wannan tallafi.

Ya kuma yi kira gare su cigaba da yimasa addu’a domin cigaba da ayyukan alkhairi.

Da take jawabi a lokacin miƙa tallafin Hajiya Asma’u Aminu Goro, tace dalilin da ya sa aka ba da wannan tallafi ga mata da marayun shine duba da yanayin da ake ciki na matsin taltalin arziki, kuma al’umma da mata suna bukatar taimakon musamman mata da suke zaune a gida.

Kotu Tsare Matashi Watanni 20 Tare Da Biyan Diyya Dubu  50, Bayan Ta Same Shi Da Laifin Saran Wani.

Ɗan Turkiyya: Yana Iƙrarin Kashe Kansa, Ya Cakawa Kansa Wuƙa Sai Naji Tsoro A  Nima Kada Ya zo Ya Cutar Dani.- Ƴar Kano.

Gwamnatin Kano Ta Kama Mushen Dabbobi A Manyanka.

Asma’u Goro, ta ƙara da cewa wannan ba shine karo na farko da ake irin wannan aikin alkhairin ba, koda yaushe Aminu Goro yana ƙoƙarin tallafawa al’ummar da yake wakilta kuma duk abinda taje masa da shi Indai na taimakone yana iya ƙoƙarinsa domin a tallafi rayuwar al’umma.

A ƙarshe ta yi kira ga wayanda suka samu tallafin da suyi amfani da shi yadda ya dace domin suma arzikinsu ya habbaka su baiwa wasu watarana.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Siyasa

2023: Ƴan Takarar Shugabancin Najeriya Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya.

Ƴan Takaran zaben shugaban kasar Najeriya da za’ayi a shekara mai zuwa, yau sun rattaba hannu akan yarjejeniyar gudanar da yakin neman zabe da kuma tabbatar da gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali. Yayin wani biki da akayi a birnin Abuja da tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar ya jagoranta, ‘yan takarar zaben da suka […]

Read More
Siyasa

Ƴan Sanda Sun Gargaɗi Masu Ɗauƙar Makamai Da Kayan Maye A Lokacin Yaƙin Neman Zaɓe.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Rundunar yan sandan jihar Kano a Arewa maso Yammacin Najeriya, ta ja hankalin yan siyasa bisa yaƙin neman zaɓe mai tsafta. Jan hankalin rundunar ya zo ne a dai dai lokacin da hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC, ta buɗe damar yaƙin neman zaɓe a hukumance. Kwamishinan ƴan sandan […]

Read More
Siyasa

Kishin Ƙasa Shi Ne Tubalin Jagorancin Al’umma, Raunin Jagoranci Shi Ke Haifar Da Rashin Adalci,-Obasanjo.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce kasar na bukatar gwamnatin da ta san yadda ake gudanar da mulki. Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito tsohon shugaban na wannan maganar a wurin taron bikin cikar makarantar Kings college ta Legas – daya daga cikin tsoffin makarantu a kasar – shekara 113 da kafuwa. Mista […]

Read More