June 27, 2022

Har Yanzu Jihar Kaduna Na Fama Da Cutar Shan Inna.

Page Visited: 286
0 0
Read Time:38 Second

Daga Ma`azu Abubakar Albarkawa

Duk da ikirarin kawar da cutar shan inna a Najeriya, an bayyana cewa akwai sauran burbushin cutar a wasu ƙananan hukumomi 7 na Jihar Kaduna.

Babban sakatare a hukumar kula da lafiya a matakin farko na jihar Kaduna Hamza Ibrahim Ikara, ne bayyana hakan wurin kaddamar da cigaba da rigakafin cutar a ƙaramar hukumar Zariya.

Ya ce ƙoƙarin hakan ne yasa gwamnati ta samar da wasu sabbin matakai domin cigaba da allurar a sassan Jihar.

Ya ƙara da cewa a jihar Kaduna ana sa ran yiwa yara miliyan biyu da dubu ɗari bakwai allurar a bana.

Hamza Ikara ya ce, ana samun sakamako mai kyau saboda shigowar sarakuna iyayen kasa wurin wayar da kan al’umma domin karɓar allurar a yankunan karkara da birane.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *