October 22, 2024

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Ina nan daram kan takarar shugabancin ƙaramar hukumar Zariya – Hamisu Idris

Ɗaya daga cikin ƴan takarar shugabancin ƙaramar hukumar Zariya ƙarƙashin inuwar jam’iyyar NNPP Hon Alhaji Hamisu Idris wanda akafi sani da Alhajin Ganda ya ce, har yanzu bai janye wa kowa a zaɓen da ke tafe ranar Asabar 19 ga watan Oktoba ba.

Ya ce labarin da ake yadawa cewa ya janye daga takarar sam babu gaskiya a ciki,wani abu ne kawai na wasu yan adawa da suka hangi faɗuwarsu zaɓe suke yi don kawo koma baya ga takarar nasa.

Ya yi kira ga al’ummar ƙaramar hukumar Zariya su yi watsi da waɗannan ƙarairayi kuma su fito a Gobe Asabar don kada kuri’ar su cikin kwanciyar hankali da lumana.

Ya nuna bukatar da ke akwai ga al’umma su zaɓe shi don muhimman manufofin da yake da shi don cigaban ilimi da lafiya da tsaro da kuma sauran abubuwan bunƙasa rayuwar al’ummar ƙaramar hukumar Zariya.

Daga nan sai Alhaji Hamisu Idris ya yi addu’ar samun gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da samun matsaloli ba.

A Gobe Asabar ne dai ake sa ran gabatar da zaɓukan ƙananan hukumomi 23 na Jihar Kaduna da Kansilolin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *