August 8, 2022

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Jahilci Da Raunin Fahimta; Mahangar Ƴan Boko Aƙida Dangane Da Shaikh Bin Fodiyo.

Page Visited: 517
0 0
Read Time:1 Minute, 11 Second

Daga Mujahid Ibraheem Eljahuny
littlemujahid4@gmail.com

Jahilci da raunin fahimta abokan juna ne. Kaɗan daga aikinsu shi ne jirkita tarihi along transformational channels, sai dai zamani da lokaci masu gadin tarihi ne, komai ƙarfin jirkicewa, lokaci da zamani za su bayyana hakika. Muna da misalai da dama kan haka.

Shortly bayan yaƙin farar hula na Amurka (American Civil War), shahararren marubucinsu wanda ke tsananin ƙaddara Tarayyar Amurka (Confederate) mai suna Jefferson Davis ya bayyana cewa ba cinikin bayi ne ya haddasa yaƙin ba, ba yawan masana tarihi a farko suna ƙaryata cewa cinikin bayi ne musabbabin yaƙin farar hular wanda aka tafka tsakanin 1861 da kuma 1865.

Da yawa suna kallon Andrew Johnson, wani ƙasurgumin ɗan adawar Harkar Neman ‘Yancin Farar Hula (Civil Rights movement) na farko farko a matsayin wani kammallen shugaba.

A yau, masana tarihi na iya fahimta cikin sauki cewa cinikin bayi shi ya haddasa wancan yaƙin, kuma shi Andrew Johnson ana kallinsa a matsayin daya daga cikin mafiya munin shugabannin ƙasa da duniya ta taɓa gani.

Waɗannan masu sukan Shehu Danfodiyo me ke damunsu in ba jahilci da raunin fahimta ba, in dai har mutum zai fahimci Shehu Danfodiyo a matsayin Bafullace, bai nisa da ya fahimci Manzon Allah (Sallahu alaihi Wa Alihi) a matsayin Balarabe, ko mai yaƙin ƙabilanci.

Turawa sun juya wa ‘yan boko akida tunani, ƙwaƙwalensu sun zama sai a hankali, ƙwaƙwalwa ta kifi! Allah ya kyauta.

Zan cigaba insha’allah…

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *