August 8, 2022

Jama’a A Yi Rijista. Kar Mata Ta Ka Da Mijin Fa!

Page Visited: 182
0 0
Read Time:3 Minute, 10 Second

Daga Dr. Aliyu U. Tilden

Ina kira ga daukacin yankasar nan, a kowane sashi suke, su yi rijista saboda kalubalen da ke tattare da zabe mai zuwa. Ga dalilaina guda uku na yin wanna kira.

Ambaliya

Sakamakon zaben fid-da-gwani na yantakarar shugaban kasa ya kawo ambaliyar masu rijistar jefa kuri’a musamman a kasashen Inyamurai da Yarbawa. Dafifin mutanen ba karami ba ne don ya sa har hukumar INEC ta kara na’urorin rijista a jihohi biyar a kasashen Inyamurai, da Jahar Legas da Jahar Kano. 5-1-1. Me wannan lissafin ya nuna maka?

Kuma me ya jawo wannan dafifi? Ina ga ba zai rasa nasaba da kokarin da kowane sashi yake yi ba ne don ya taimaka wa nasa dantakarar da kuri’u don idan kowanne zai sa daukacin masu jefa kuri’a a sashinsa su fito, ba shakka likkafarsa za ta ja gaba.

A nan, yan’arewa suna da matsalar ko-oho (complacency) ganin cewa suna da yawa. Ina ga wannan babban kusukure ne. Jefa kuri’a a yau ya zama wajibi ga duk wanda yake son ya ga an samu cigaba a kan abin da ya dame shi. Yau muna cikin tasku na rashin zaman lafiya. Ya kamata a ce mun fi kowa damuwa da waye zai zama shugaban kasa saboda shi ne zai shugabanci hukumomin tsaro gaba daya. Idan wani zai yi amfani da su ya taimake mu, wani zai iya amfani da su ya cutar da mu.

In mun yi cakulatin-bangwaro da zabe mai zuwa, yana yiyuwa abubuwa su kara tabarbarewa har inda fitinar bata kai ba yau ta kai gobe, ko a bullo da wasu sabbin fitinun. Su ma sauran sassan kasar suna da abubuwan da ke damunsu kuma a kan haka za su jefa kuri’a. To me zai sa ba za mu himmatu ba kamar yadda suke nuna himma a kwanakin nan?

Tuwon Gobe

Na yarda akwai mutane da yawa da rashin kyan mulkin Buhari ya kashe wa guiwa. Ga mai hankali, wannan shi ne ma zai sa a kara himma, a gwada wani, watakila a yi dace; ana zaton wuta a makera, a same ta a masaka. Ala ayyi halin, mu yankasa mu yi namu. Mu zaba. Idan wadanda muka zaban suka ci amanarmu ko suka gaza sai mu bar su da Allah. Rashin dadin tuwon yau ba shi zai hana mu cin na gobe ba.

Ingancin Zabe

Bugu da kari, yau kuri’a tana da muhimmanci ba kamar a baya ba don anci karfin magudi a lokacin zabe. Wannan cigaba ya samu ne don rijistar masu jefa kuri’a da aka samar tun zamanin marigayi Yar’adua (Allah ya masa rahama), da amfani da fasahohin zamani na tantance masu jefa kuri’a, da aikawa da sakamako daga mazabu kai tsaye zuwa rumbun bayanai na INEC, da kuma uwa-uba dokoki dabam dabam da ke cikin dokokin zabe da aka kafa tun 2011.

Yau idan mutum ya jefa kuri’a akwai tabbaci mai rinjaye cewa za a kirga ta a yawan kuri’un dantakarar da ya jefawa. Me ya fi haka dadi? Ba a gama seta komi da komi ba, amma dai an ci karfin magudi. Wanda aka tafka a shekarun baya ba za a sake iya yinsa ba yanzu. Don haka wadanda da suke cewa kuri’arsu ba ta da amfani yakamata su bar wannan turbar, su fara yin zabe.

Sakiyar Da Ba Ruwa

Don wadannan dalilai, ina kira ga kowa ya tsaya kan wadanda yake da iko a kansu ko wadanda suke jin maganarsa ya tabbatar da kowannensu ya yi rijista. Kuma idan lokacin zabe ya zo kowa ya jefa kuri’arsa ga wanda ya fi zaton zai fi alheri da kawo cigaba a kasa.

Wannan sako ne mai muhimmanci. Don Allah a kula.

Dr. Aliyu U. Tilde
12 Yuni 2022

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *