Jami’an Tsaro Sun Gano Jaririn Da Aka Sace Kusan Mako Guda A Wani Asibitin Jihar Bauchi.

Page Visited: 1657
0 0
Read Time:1 Minute, 24 Second

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Hukumar asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, da ke jihar Bauchi a Arewacin Najeriya, ta ce an gano jaririn da aka sace a asibitin a makon jiya.

Dr. Haruna Liman mataimakin shugaban asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewan, yace an samu jaririn ne cikin daren ranar Litinin da misalin ƙarfe 1 na dare.

Da yake tabbatar da samun jaririn ya ce an samu jaririn ne sakamakon haɗin kai da jami’an tsaro.

Da yake miƙa jaririn da mahaifiyar sa Haruna Liman, ya ce ba shakka dole ne su godewa Allah domin a cewar samun jaririn ba ƙaramar nasara bace wanda kuma an miƙa shi ga mahaifiyarsa cikin koshin lafiya.

Ya kuma ce an samu jaririnne bayan ƙoƙarin jami’an Tsaron asibitin dana sauran jami’an tsaro da suke Bauchi.

Ibrahim ɗan lami Khalid mazaunin garin buzaye a ƙaramar hukumar Bauchi shine mahafin jariran biyu da aka sace dayan su, ya ce lokacin da aka sace jaririn ya shiga fargaba gami da tashin hankali, to amma yanzu ya samu farin ciki da samun jaririn.

ya kuma miƙa godiyar sa ga jami’an tsaro bisa kokarin da suka yi na gano ɗan nasa da aka sace cikin kwanaki shida.

Mahaifiyar jaririn Malama Bilkisu, da a baya ta shiga cikin wani yanayi na dimauta sakamakon sace jaririn yanzu ta dawo hayyacinta cikin farin ciki, wadda a baya ko bacci bata iya yi.

Zuwa yanzu wadda ake zargi da sace jaririn da tana hannun jami’an tsaro da ke suke cigaba da binkarta kamar yadda hukumar Asibitin ta bayyana.

An sace jaririn ne a ranar Larabar makon jiya wanda aka haife su tagwaye, sace jaririn dai ya tayar da hankalin yan uwa da abokan arziki.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Mayan Titunan Jihar Kano Da Gwamnati Ta Haramtawa Masu Adaidata Sahu Bi.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Gwamnatin jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya  ta haramta wa Ƴan Adaidaita Sahun bin wasu manyan titunan jihar baki ɗaya. Gwamnatin ta ɗauki matakin ne ta hannun  Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jihar KAROTA. Sanarwar dokar ya fito ne cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in hulɗa […]

Read More
Labarai

An Koyar Da Gwamman Matasa Kiwon Tumaki A Jihar Bauchi.

Daga Muhammad Sani Mu’azu Kimanin matasa maza da mata 35 ne aka horar kan dabarun kiwon tumaki, don dogaro da kansu da kuma yaki da talauci. Taron wanda kamfanin Ivie General Contractors da cibiyar kimiyyar dabbobi ta Najeriya ta shirya karkashin tsarinta na samar da abin yi wa marassa galihu a bangaren kiwon dabbobi a […]

Read More
Labarai

NUBASS: A karon Farko an samu Shugaban Ɗalibai ƴan asalin jihar Bauchi na kasa daga Jami’a mallakar Jiha

  Kwamitin gudanar da zaɓen Ƙungiyar ɗalibai ƴan asalin jihar Bauchi wato NUBASS a matakin ƙasa ta gudanar da zaɓen ta wanda ta sabayi duk shekara. Shugaban kwamitin zaɓen Kwamaret Abdullahi ya bayyana zaɓen a matsayin wanda ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana la’akari da irin yadda ɗalibai suka bada haɗin kai har akayi […]

Read More