January 31, 2023

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Jami’an Tsaro Sun Hallaka Ƴan Bidinga Tare Da Ragargaza Maɓoyarsu.

Page Visited: 67
0 0
Read Time:1 Minute, 28 Second

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Rundunar yan sandan jihar Bauchi da ke gabashin kasar nan, haɗin gwiwa da kungiyoyi, wasu hukumomin tsaro sunce sun hallaka yan bindiga tare da ragargaza sansaninsu a karamar hukumar Alkaleri da ke jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ƴan sandan suka fitar mai dauke da sa hannun kakakinta SP Ahamad Muhammmad Wakil.

Sanarwar mai dauke da sa hannun kakakin yan sandan sifiritandan yan sanda Ahmed Muhammed Wakil, ta ce hadin kai da aka samu tsakanin yan sandan da sauran kungiyoyin tsaro, ya sa sun hallaka masu garkuwa da mutane da yan bindiga gami da ruguza maboyarsu da ke dajin Madam na Yankari.

Wakil ya kuma ce jami’an tsaro sun kai samamenne cikin dajin domin kama ƴan bindigar waɗanda wasunsu suka ara ana kare, inda suka yi nasarar kwace wasu bindigogi a hannunsu kiran AK47.

A wani labari makamanci haka kuwa, rundunar ta ce jami’anta tare da hadin gwaiwar sashin da ke yaƙi da masu garkuwa da mutane sun cafke wasu masu garkuwa da mutane guda 2.

Wadana da ake zargin sun hada Adamu Muhammad, dan shekaru 33 da haihuwa wanda aka kamashi tare da wani mai suna Datti, sai kuma wani Alhaji Bulama, dan shekara 35 a yankin Maimadi na gundumar Pali.

Yan sandan sunce bincikensu ya nuna cewa babba cikin wadanda ake zargin shine Adamu Muhammad, ya bayyana da bakinsa cewa yana cikin wadanda suka yi garkuwa da mutanen a kauyen Kaltanga, inda sukabyi garkuwa da mutum 4 suka kuma ajiyesu a dajin Yankari har tsawon 5 kancewa har sai an ba da naira miliyan 20 kudin fansa kafin su sakesu.

Rundunar yan sandan ta ce zuwa yanzu tana cigaba da gudanar da bincike daga ta kamala za ta gurfanar da waɗanda ake zargin gaban kotu.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *