August 8, 2022

Jam’iyyar APC Tsagin Shekarau Sun Mika Koken su Ga Kwamitin Sasanci.

Page Visited: 2854
0 0
Read Time:1 Minute, 12 Second

Daga: Comr Aliyu Abdul Garo

A ranar litinin kwamitin sasanci da bin bahasi da uwar jam’iyyar APC ta kasa ta kafa karkashin jagorancin gwamna Mai Mala Buni, wanda Sanata Abdullahi Adamu, tsohon gwamnan jihar Nassarawa, yake shugabanta ya samu zama a jihar Kano domin karfar korafin bangaren sanatan Kano Malam Ibrahim Shekarau.

Ƴan kwamitin da sun hada da Barista Ali Sa’adu Birnin Kudu da Alhaji Sulaiman Argungu da tsohon gwamnan Enugu Sullivan Chime da tsohon kakakin majalisar tarayya Yakubu Dogara da tsohon gwamnan Binuwai George Akume da Moses Adeyemi a matsayin sakataren, sai tsohuwar mataimakiyar gwamnan Lagos Oluranti Adebule, da kwamishinan lafiya na jihar Cross River Beta Edu.

, shi ne ya jagoranci wannan bangare, wanda ke tare da Sanata Barau I. Jibrin da Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe da Hon. Nasir Abduwa Gabasawa da Hon. Haruna Isa Dederi da Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada da kuma Alhaji Shehu Dalhatu.

A yayin zaman sanata Malam Ibrahim Shekarau, a madadin sauran jam’iyyar APC na Kano wandanda suke tsagin sa son ya gabatar da dunkullallen kukan ‘yan APC ga kwamitin.
‘Yan kwamitin sun saurari duk bayanai na baka da hujjoji na rediyo da bidiyo kuma sun karbi roko da bukatun wannan tsagin ya gabatar da dunkullallen kukan ‘yan APC ga kwamitin.

Bayan zama da bangaren Sanata Malam Ibrahim Shekarau, kwamitin zai gana da mutanen gwamnatin gwamna Abdullah Umar Ganduje.

Daga bisani kwamitin zai samu wata mahada da za a yi tattaunawa gemu da gemu da duk bangarorin.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *