Daga www.facebook.com/macbash1067
Kabilu da dama a fadin Duniya suna daukar tofawa mutum yawu ko majina a matsayin cin zarafi; kaskantarwa ko kuma kazanta.
Sai dai abin ba haka yake ba a wurin kabilar Massai, wadanda ake yawan samun su a yankunan kasashen Kenya da Tanzania – duk a Nahiyar Afrika. A wurin su yana nufin gaisuwa da sanya albarka da gimamawa da martabawa da kuma karramawa.
Wadannan al’uma, duk da cewa yawan su a gaba daya wadannan kasashen guda biyu bai haura kaso daya cikin dari ba; tasirin da suke dashi da kuma shuhura ya girmama – domin kuma har ana zuwa yankunan su domin yawon bude idanu.
Har ma ta kai ga masu shirya fina-finai na Nahiyar Afrika da dama, sukan kwaikwayi yanayin al’adunsu; suna nuna wa a cikin shirye-shiryen su – kamar yadda aka nuna a cikin wani shahararren fim na “the gods must be crazy” na farko da kuma na biyu.
Abinda Yasa Kabilar Massai Suke Tofin Yawu Da Majina
Mafi yawan al’umar kasar Tanzania na gidi – ko kuma ‘yan asalin kasar, sukan tofe hannayen su a duk lokacin da suka nufaci gaisawa da mutum – wato idan mutum zai yi musafaha da dan’uwansa, sai ya mulke hannunsa tsaf da yawu da majina; kafin ya mikawa dan’uwansa – wanda shima tuni ya mulke na sa hannun.
Yin hakan, a wurin su, shine makurar girmamawa da kuma ladabi da biyayya da kauna – kuma ba kowa ma ake yiwa haka ba – sai wanda matsayin sa ya kai matsayin gaske.
Haka nan, al’adar wannan kabila ta Massai itace; a duk lokacin da akace mace ta haifi jariri – to haramun aji wani yana faadin abin alheri game da jaririn ko kuma aji yana yi masa fatan alheri a rayuwa…maimakon haka, sai dai a rika janyowa jaririn muggan alkaba’i da masifa da bala’i – a ganin su hakan shine kadai zai sa jaririn ya samu rayuwa mai kyau idan ya girma.
Bayan an gama yiwa jariri wadannan kalamai kuma, sai mutane kowa yazo; ya rika tofe wannan jariri da yawu da majina – da zummar cewa a haka ne yaron zai yi albarka da nasibi a rayuwarsa – kuma ba zai mutu da wuri ba.
Idan kuma akace an wayi gari wani daga cikin kabilar yana aurar da diyar sa – wato yar sa, to a al’adar sai mahaifin ta yazo; ya tofe mata goshin tsaf da yawu da majina; sa’annan kuma ya tofa mata yawu akan nonon ta, a matsayin sanya albarka da kuma fatan samun zuri’a.
Wadannan mutane da ake kira kabilar Massai dai suna da saukin rayuwa, kuma mafi akasarin su manoma ne – sa’annan wadanda a cikin su ba sa noma, suna taimakawa masu yawon bude ido ne wurin nuna masu wurare.
Ana yawan gane yan kabilar Massai ne da wadansu duwatsu da suka sanyawa a kugun su da kuma wuyayen su – hadi da rawani ko kuma nadi. Mazan su da matan su kuma akwai wani kaya da suke yin ado dashi, wanda ake kira da Shuka.
Shin za ku iya hada dangi da yan Kabilar Massai masu tofi?
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Shanun Sun Yi Zanga-zangar Ce Don Rashin Cika Alƙawuran Gwamnati A Indiya.
-
Ana Ƙoƙarin Ceto Rayukan Kifaye Sama 100 A Australia.
-
Budurwar Ta Kai Kanta Ga Ƴan Sanda Ne Bayan Saurayin Ta Ɗan Ƙasar Turkiyya Na Neman Ta Ruwa A Jallo.
-
Ango Da Amaryar Da Aƙali Ya Aike Su Gidan Ɗan Kande Bayan Zargin Azabtar Da Ɗan Kishiyarta.
-
Bauchi: Amarya Da Ango Za Su Ci Amarci A Gidan Yari