December 2, 2021

Kamfanin Jirgin Saman Najeriya Zai Fara Aiki Shekara Mai Zuwa.

Page Visited: 536
0 0
Read Time:31 Second

Gwamnatin Najeriya tace sabon kamfanin jiragen ta da aka yiwa suna Nigeria Air zai fara aiki daga watan Afrilun shekara mai zuwa bayan dogon tsaikon da aka samu.

Kafafen watsa labarai su rawaito ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya sanar da cewar wani kamfani ne zai kula da hada hadar jiragen, wanda gwamnati zata zuba jarin kashi 5 a cikin sa, sai kuma wasu ‘yan kasuwar zasu zuba kashi 46, yayin da za’a sayarwa sauran mutane masu bukatar sanya hannun jari kashi 49.

Hadi yace idan kamfanin ya fara aiki zai samar da ayyukan yin ga mutanen da zasu kai 70,000.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *