Daga Suleman Ibrahim Moddibo
Rundunar ƴan sandan jihar Kano a Arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta kuɓutar da yara ƴan mari 113 da ake tsare da su a wani gida da ke unguwar Na’ibawa Ƴan Lemo a ƙaramar hukumar Kunbutso.
Rundunar ƴan sandan ta ce tayi nasarar kuɓutar da ƴan marin ne bayan samun rahoto daga wasu mutum goma, da suka kuɓuta daga cibiyar gyaran hali ta wani Musa Safiyanu mai shekaru 55, mazaunin unguwar ta Na’ibawa, wanda yake gudanar da cibiyar ba bisa ƙa’ida ba, cewa yana kulle yara tare da azabtar da su.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce bayan ƴan sanda sun samu ƙorafin ne kwamishinan ƴan sandan jihar Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya bayar da umarnin bincike kan lamarin inda bayan haka ne su ka yi nasarar tseratar da yara 113 da aka kulle su a wani daki.
Ya kuma ce cikin waɗanda aka tseratar ɗin akwai waɗanda aka samu su da raunuka wanda tini a kai su babban asibitin Murtala Muhammad da ke Kano domin kula da lafiyar su, tare da miƙa su ga gwamnatin jihar Kano.
Ana kuma zargin cikin a yaran da ake tsare da su akwai wani guda da ya rasa ransa sakamakon dukan da ɗaya daga cikin yaran malamin yayi masa.
Gwamnatin Kano Za Ta Tono Gawar Wani Yaro Da Ake Zargin Malamin Su Ya Kashe Shi.
Mutum 6 da ake zargin bincike ya nuna suna gudanar da cibiyar tsahon shekara 10, wanda tini gwamnatin jihar Kano ta haramta yin gidan mari a jihar.
Kiyawa ya ce zuwa yanzu kwamishinan ƴan sandan Kano ya bayar da umarnin gudanar da bincike, kuma da an kammala za a gurfanar da waɗanda ake zargin gaban kotu.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Kotu Ta Daure Wani Matashi Watanni 15 Kan Shiga Gidan Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi M.A.
-
Amaryar Ta Rasa Idonta Daya Ne Ana Tsaka Da Bikinta Sai Dai Duk Da Haka An Daura Mata Aure Da Angonta.
-
Zargin Taimakawa Ta’addanci: SSS Sun Mamaye Hedikwatar Babban Bankin Najeriya.
-
Gwamna Bala ya sha alwashin inganta tsaro, yaƙi da talauci, yayi yaƙin neman zaɓe a Itas
-
Ciyar Da Jihar Bauchi Gaba Ne Muradin Mu, Ku Sake Ba Mu Dama – Saƙon Gwamna Bala Ga Al’umar Udubo