Daga Suleman Ibrahim Moddibo
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama mutum 4 da ake zargin su da yin fashi da makami a unguwar Western Bypass na karamar hukumar Kunbutso a jihar Kano.
Waɗanda ake zargin dun haɗa da Hussaini Hassan, mai shekaru 21 wanda ke zaune a unguwar Zoo Road sa kuma shugaban su Ali Isah, wanda aka fi sani da “Aljan”, ɗan shekaru 39 da ke zaune a unguwar Tudun Murtala, sai sauran biyun da suka haɗa da Ismail JL, mai shekara 42 mazaunin Sabon Gari, da kuma Rabiu Ibrahim, mai shekara 38 da haihuwa, ɗan unguwar Hotoro, dukkan su a jihar Kano.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano da ke Arewa maso yammacin Najeriya DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da kama waɗanda ake zargin tun ranar 7 ga watan 1 na wannan shekara ta 2022.
Kiyawa ya ce bayan samun wannan ƙorafi kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano Sama’ila Sha’aibu Dikko ya tura dakarun ƴan sanda zuwa nan unguwa da gaggawa “muka samu nasarar kama mutum ɗaya wanda ƴan unguwa su kai masa tara-tara jina-jina mun ɗauke shi da gaggawa mun tafi da shi babban asibitin Murtala da ke nan cikin garin Kano wanda daga baya kuma aka duƙufa kan bincike.”
Ya kuma ce “daga binciken farko an kama shi da wayoyi wanda akai fashin su guda biyu hakazalika da aka faɗaɗa bincike an samu nasarar sauran abokanan sa mutum uku da akai fashin da su sun zo hannu.”
Yanzu haka dai kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano ya ba da umarnin a gurfanar da su a gaban kotu domin ayi musu hukunci,” a cewar Kiyawa.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Tsaro : Ƴan IPOB sun ƙone sakatariyar Ƙaramar Hukuma a jihar Anambra.
-
Ukraine :Rasha ta gargadi kamfanin Google.
-
Rasha-Ukraine: Rukuni na farko na ƴan Nijeriya sun isa Abuja.
-
Kotu: Abduljabar Ya Rantse Da Alƙur’ani Bai Aikata Laifukan Da Ake Tuhumarsa Da Su Ba.
-
Da Dumi Dumi :Gomnatin tarayya ta amince ta mika Abba Kyari wa Amurka.