January 19, 2022

Kano: Jaafar Jaafar Ya Raba Kyautar Miliyan Daya Ga Marasa Galihu.

Page Visited: 557
0 0
Read Time:1 Minute, 6 Second

Dan Jaridar nan Jaafar Jaafar mawallafin Daily Nigerian ya taimakawa sama da mutane 40 da suka fito daga sassa daban daban na jahar Kano da kuɗaɗe domin samun lafiya da kuma ilimi.

Wasu daga cikin mutanen da suka samu tallafi suna bukatar ayi musu tiyata ne a wasu asibitoci amma ba su samu kudin ba biya , wasu kuma magunguna aka rubuta musu amma babu kudin siya, wasunsu kuma dalibaine na manyan makarantu za su biya kudin makaranta amma ba su da shi, saboda haka Jaafar Jaafar ya taimaka musu.

A kwanakin baya ne dai wata kotu ta umarci Gwamnan Kano da ya biya Jaafar Naira dubu dari takwas (N800,000) sabo da bata mishi lokaci da gwamnan ya yi akan shari’ar da ta shafi bidiyon dollar.

Bayan karbar wannan kudin ne sai Jaafar ya cika Naira dubu dari biyu (N200,000) su ka zama miliyan daya, ya kuma mikasu ga sashen Inda Ranka na Freedom Radio domin a zabo daga cikin mabukata da su ke zuwa neman taimako akan matsalolin lafiya da na ilimi, a share musu kukansu.

Jaafar Jaafar dai yanzu haka Jaafar da iyalansa su na gudun hijira a kasar Birtaniya sakamakon barazana da ya sha fama da ita akan fallasa bidiyon da ke zargin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yana karba dololin Amurka yana sanya su cikin aljihu.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *