Daga Ummahani Ahmad Usman
Rudunar yan sandan jihar Kano da ke Arewcin Najeriya ta sanar da mutuwar wata matashiya mai suna Sadiya Usman, yar shekara 16 wadda ta rataye kanta cikin daki a kauyen Garin Dau da ke karamar hukumar Warawa.
Kakakin rudunar yan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya sanar da hakan ga manema labarai inda yace, “ranar daya ga watan 8 na wannan shekara ta 2022 da miasalin karfe uku da munti 45 a yamma, mun samu kira daga dagaci Garin Dau karamar hukumar Warawa a nan jihar Kano, a kan cewa wata matshiya mai suna Sadiya Usman yar kimanin shekara 16 ta rataye kanta a cikin daki,”
A cewa rudunar bayan samun rahoton ne mataimakin kwamishinan yan sandan jihar DCP Abubakar Zubairu, ya aike yan sanda da gaggawa domin a kaita asibiti “wanda suka je wannan guri da gaggawa suka sameta a rataye, inda ta yi amfani da turame guda biyu da kuma gyale da dan kwalinta, an garzaya da ita babban asibitin Wulin inda babban likita ya tabbar da cewa ta rasu, yanzu haka dai an dukufa domin gudanar da bincike a kan wannan lamari,” in ji Kiyawa.
Gwamnatin Kano Ta Yiwa Sheikh Qaribullahi Kabara Kyautar Fili.
Kano: Ƴan Sanda Sun Kwace Kwayar Tramadol Kimanin Ta Naira Miliyan Ashirin Da Biyar.
YAPS Na Son Gwamnatin Kano Ta Yi Kwamishinan Tsaro Da Harkokin Cikin Gida A Jihar.
Ana dai yawan samun rahotanni kan mutanen da ke kashe kansu a jihar kano wanda wasu ke alakanta hakan da cutar damuwa, to sai dai a baya-bayan nan hakan ya ragu kila dan yadda ake wayar da kan mutane kan illar da ke tare da kashe kai.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Fararen Hula Na Cikin Mawuyacin Hali A Sudan.
-
Kwacen Waya: Zamu Kori Masu Siyen Wayar Sata Daga Kasuwar Mu- Farm Center.
-
Sojoji Sun Kashe Wani Fitaccen Ɗan Bindiga A Kaduna.
-
Rundunar Ƴan Sandan Jihar Kano Ta Gargadi Mazauna Jihar Kan Atisayen Harbin Bindiga A Kalebawa.
-
Ba Zamu Lamunci Daba Da Shaye-Shaye A Unguwarmu Ba- Al`Ummar Dala.