Kano: Rundunar Yan Sanda Ta Gargaɗi Mazauna Jihar Da Ke Yaɗa Labaran Ƙarya Kan Tsaro.

Page Visited: 82
0 0
Read Time:1 Minute, 16 Second

 

Da take kore raɗe-raɗin ganin wasu da akai zargin ƴan ta’adda ne da suka kai su kimanin su ɗari bisa babura a wata unguwa mai suna Kuntau da ke Kano, rundunar ƴan sandan jihar ta gargadi masu yaɗa labaran ƙarya kan abinda ya shafi tsaro da ahir ɗin su.

Tana mai cewa tsaro muhimmin abu ne da ba a wasa dashi don haka daga an ga wani abu ya kamata a an ƙarar da jam’an tsaro ba wai a je Soshiyal Midiya ana yaɗawa ba.

Da yake wa manema labarai karin haske kan rahoton Sifiritandan ƴan sanda Abdullahi Haruna Kiyawa ya ƙaryata cewa an ga ƴan ta’addan da wata mata tayi iƙrarin gani yana mai bayyana irin rahoton da suka samu.

“A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne dai aka samu labarin waɗansu mutane su shida sun shiga unguwar Yamadawa, Kuntau da misalin karfe 10 na dare wanda ake kyautata zaton yan ta’addane akan babura masu kafa biyu.”

Ya kuma ce, binciken farko ya tabbatar da cewa mutanan ba yan ta’adda bane yan uwan wani bawan Allah ne da suka kai masa ziyara unguwar.

Kiyawa ya ƙara da cewar, jita-jitar da take ta yawo a kafafan sada zumunta na Facebook kan cewa an ga babura kimanin guda 100 da goyon uku uku sun shiga anguwar ba gaskiya bane, inda Ya kara tabbatar da cewa hakan jita-jita ne kawai da ake yaɗawa.

daga karshe ya ja hankalin al’umma da su gujewa yaɗa jita-jita kan abinda ya shafi tsaro.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Mayan Titunan Jihar Kano Da Gwamnati Ta Haramtawa Masu Adaidata Sahu Bi.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Gwamnatin jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya  ta haramta wa Ƴan Adaidaita Sahun bin wasu manyan titunan jihar baki ɗaya. Gwamnatin ta ɗauki matakin ne ta hannun  Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jihar KAROTA. Sanarwar dokar ya fito ne cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in hulɗa […]

Read More
Labarai

An Koyar Da Gwamman Matasa Kiwon Tumaki A Jihar Bauchi.

Daga Muhammad Sani Mu’azu Kimanin matasa maza da mata 35 ne aka horar kan dabarun kiwon tumaki, don dogaro da kansu da kuma yaki da talauci. Taron wanda kamfanin Ivie General Contractors da cibiyar kimiyyar dabbobi ta Najeriya ta shirya karkashin tsarinta na samar da abin yi wa marassa galihu a bangaren kiwon dabbobi a […]

Read More
Labarai

NUBASS: A karon Farko an samu Shugaban Ɗalibai ƴan asalin jihar Bauchi na kasa daga Jami’a mallakar Jiha

  Kwamitin gudanar da zaɓen Ƙungiyar ɗalibai ƴan asalin jihar Bauchi wato NUBASS a matakin ƙasa ta gudanar da zaɓen ta wanda ta sabayi duk shekara. Shugaban kwamitin zaɓen Kwamaret Abdullahi ya bayyana zaɓen a matsayin wanda ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana la’akari da irin yadda ɗalibai suka bada haɗin kai har akayi […]

Read More