June 8, 2023

KAROTA Ta Kama Wani Matashi Da Ke Sojan Gona Da Sunanta.

Page Visited: 1265
0 0
Read Time:1 Minute, 13 Second

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta cafke wani matashi yana sojan-gona da hukumar.

KAROTA, ta sanar da kama  hakan ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa, inda ta ce, ta cafke matashin ne dai-dai lokacin da yake tsaka da tare motoci akan titi sha biyu na daran ranar Litinin.

“Matashin mai suna Lukman Abdullahi mai shekaru 27 mazaunin unguwar Sabon Gari bayan kama shi ya bayyana cewa shi ɗan Maiduguri ne,” in ji sanarwar.

Shugaban Hukamar Karota Na Jihar Kano Ya Kasa Bayyana A Gaban Kotu.

Gwamnatin Kano Ta Yiwa Sheikh Qaribullahi Kabara Kyautar Fili.

‘Yan Sanda Sun Kama Mutum 40 Bisa Zarginsu Da Tashin Hankalin Al`umma Da Sunan Yajin Aikin Masu Adaidaita Sahu A Kano.

Nabilusi ya kuma ce, matashin yana amfani da kayan ne saboda jama’a su fahimci shi ma’aikacin hukumar ne.

“hukumar ta jima da samun rahoton yadda matashin yake amfani da yawunta wajen cusgunawa al’umma, wanda sai a wannan karon dubunsa ta cika.”

shugaban Hukumar ta KAROTA Baffa Babba Ɗan’agundi ya shawarci al’umma da su cigaba da kai rahoton duk wani jami’in da suka ga yana karɓar cin-hanci domin ya fuskanci tuhuma, cewar sanarwar.

Nabulusi ya kara da cewa idan suka kammala binke akansa zasu miƙa shi hannun jami’an Yansanda domin faɗaɗa bincike tare da gurfanar da shi a gaban kotu domin fuskantar tuhuma.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *