December 2, 2021

Kasar Saudi ta yanke hukunci kan aikin hajjin bana.

Page Visited: 323
0 0
Read Time:33 Second

Daga: Muhammad Sani Mu’azu.

Gwamnatin kasar Saudiyya tace mazauna kasar ne kadai zasu samu damar aiwatar da aikin Hajjin bana.

Sanarwa daga ma’aikatar aikin Hajji kasar ta ce an dauki wannan mataki ne bisa la’akari da yadda cutar COVID-19 ta yadu zuwa kasashe sama da dari da tamanin a fadin duniya, da kuma adadin mutanen da suka rasa rayukan su sanadiyar wannan annoba.

Kasar saudiyya ta ce za’ayi aikin hajjin tare da bin duk wasu hanyoyin da aka ayyana na kare kai daga kamuwa da wannan annoba.

Sannan za’a bayar da tazara a lokacin aikin Hajjin kuma za’a gudanar da shi bisa koyarwar addinin musulunci kamar yadda aka saba.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *