August 8, 2022

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Kimanin Mutane Dari Biyar Za Su Ci Gajiyar Tallafin Sa’adatu Bello A Ƙaramar Hukumar Kirfi.

Page Visited: 651
0 0
Read Time:1 Minute, 9 Second

Kwamishinar kananan masana’antu ta jihar Bauchi, Hon. Sa’adatu Bello Kirfi ta baiwa mata ɗari biyu tallafin dubu biyar- biyar domin inganta ƙananan sana’o’i a ƙaramar hukumar Kirfi.

D yake ƙarin haske kan shirin mai taken Hon. Sa’adatu Bello Micro Economic Empowerment Programme  (SBKMEEP) a turance, Malam Bello Ahmad Kirfi, ya ce kimanin mutane ɗari biyar ne za su ci gajiyarsa a faɗin ƙaramar hukumar Kirfi, wanda  turmin farko mata ɗari biyu za su amfana.

A da ya ke gabatar da jawabinsa Sarkin Kirfi, Alhaji Kawuji Garba Kirfi, ya yabawa kwamishinar Sa’adatu Kirfi, kan irin hubbasa da ta ke yi wajen kawo ci gaba ga ƙaramar hukumar Kirfi a fannoni dabam-dabam.

A nasa jawabin wakilin Wamban Bauchi, hakimin ƙasar Kirfi Alhaji Adamu Mu’azu, ya bayyana kwamishinar a matsayin magajiyar Baba Wazirin Bauchi, Alhaji Muhammadu Bello Kirfi, tare da yaba mata kan irin ayyukan alheri da ta ke kaiwa ƙaramar hukumar Kirfi.

Shugaban ƙaramar hukumar Kirfi wanda ya samu  wakilcin muƙƙadashinsa Alhaji Sulaiman Adamu Cheledi, ya ce Hon. Sa’adatu Bello Kirfi  mace ce mai kamar maza ya kuma yi mata fatan alheri.

Da take ƙaddamar da shirin, Hon. Sa’adatu Bello Kirfi, ta godewa al’ummar ƙaramar hukumar Kirfi, bisa irin goyon baya da suke bata tare da gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed.

“Haƙiƙa ina jin daɗin irin gudunmawa da goyon baya da kuke bani ƙarkashin jagorancin gwamna Bala Abdulkadir Mohammed,” a cewar kwamishinar.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *