Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto a yau Litinin ya sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 da aka kafa a babban birnin Sokoto ranar Asabar.
Yanzu dai an sassauta dokar ta zama daga magariba zuwa wayewar gari.
Gwamnan ya sanya dokar ta-ɓacin ne domin shawo kan tashe-tashen hankula da suka biyo bayan kisan da aka yi wa wata dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato da ke karatu a ajin 200 bisa zargin furta kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW).
Ɗage dokar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai, Alhaji Isa Bajini-Galadanchi ya fitar.
Ya bayyana cewa sassauta dokar hana fitar ya biyo bayan bayanan da hukumomin tsaro suka bayar a jihar.
Ya ƙara da cewa “an sassauta dokar ne don baiwa mutane damar gudanar da kasuwancinsu na halal da sauran harkojin rayuwa,” in ji shi.
Kwamishinan ya ruwaito Gwamna Tambuwal yana shawartar mazauna yankin da su zauna lafiya tare da gargadin cewa gwamnati ba za ta lamunci karya doka ba.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
An Yi Ƙarar Buhari Kan Batan Kuɗin Wutar Lantarki Naira Tiriliyan 11.An Yi Ƙarar Buhari Kan Batan Kuɗin Wutar Lantarki Naira Tiriliyan 11.
-
Zamu Rufe Tashoshin Jirgin Sama Dana Ƙasa Da Titunan Idan Ba’a Janye Yajin Aikin ASUU – Ɗalibai.
-
Gwamnati Ta Ayyana Masu Amfani Da Makami Suna Kwacen Waya Amatsayin Yan Fashi- YAPS.
-
Yadda muka tsira daga sansanin ƴan ta’adda tareda ƴaƴan mu – Ƴan matan Chibok da suka kuɓuta.
-
Gaskiyar Bidiyon Ɗan Najeriyar Da Ya Yi Kuka A Raudar Annabi, Wanda Hakan Ya Jawo Ce-Ce-Ku-Ce.