August 8, 2022

Kotu Ta Aike Da Tsohon Babban Akanta Janar Ahmed Idris Da Mutum Biyu Gidan Yarin Kuje.

Page Visited: 1132
0 0
Read Time:45 Second

Wata babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, babban birnin Najeriya ta bayar da umarnin tsare tsohon babban Akanta Janar na kasar Ahmed Idris a gidan yarin Kuje.

BBC Hausa ta rawaito cewar, kotun ta bayar da umarnin kai Mista Idris kurkukun ne bayan hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon-kasa, EFCC, ta gurfanar da shi da mutane biyu da kuma wani kamfani a gabanta ranar Juma’a bisa zargin su da sata da kuma zamba-cikin-aminci ta kimanin Naira biliyan 109.

Mutanen da aka gurfanar a gaban kotun su ne Ahmed Idris, Godfrey Olusegun Akindele, Mohammed Usman da kamfanin Gezawa Commodity Market and Exchange Limited.

A watan Mayun da ya gabata ne EFCC ta kama babban Akanta Janar na kasar bayan ya ƙi amsa gayyatar da ta riƙa aika masa domin tuhumarsa kan zarge-zargen da take yi masa, kamar yadda hukumar ta bayyana.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *