January 31, 2023

Kotu Ta Daure Wani Matashi Watanni 15 Kan Shiga Gidan Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi M.A.

Page Visited: 62
0 0
Read Time:46 Second

Daga Fa`izu Muhammad Magaji

Wata kotun addinin Musulunci mai lamba biyu da ke zama a Tashar Babiye a birnin Bauchi, ta daure wani matashi Abubakar Sadik, mazaunin A A Waziri da ke Bauchi, bayan samun sa da laifin shiga gidan tsohon gwaman jihar Bauchi Barrister Abdullahi Abubakar M.A, ba tare da izini ba, har ta kai ga ya yi sata a gidan.

Matashin wanda rundunar yan sandan jihar Bauchi ta gurfanar da shi a gaban kotu an zarge shine da shiga gidan tsohon gwamanan ba da izini ba, inda kuma ya sace na`urar sanyaya daki, zargin matshin ya amsa aikatawa a gaban kotu.

Bayan amsa laifinsa Alkalin kotun mai shari’a Barrister Muktar Adamu Bello Dambam, ya yankewa matashin hukuncin daurin watanni 15 gidan gyaran hali, ko kuma biyan naira dubu Ashirin da Biyar, ya kuma ba da umurni, mayar da kayan da matshin ya sata ga mai su nan take.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *