Labarai
Trending

Kotu Ta Haramtawa Gwamnatin Kano Shiga Filin Idi Tare Da Cin Tararta Biliyan 30.

Babbar kotun Tarayya da ke zaman ta a Gyaɗi-gyaɗi a Kano ta umarci Gwamnatin jihar ta biya ƴan Kassuwar da ke da shaguna a filin Masallacin Idi da ke Ƙofar Mata Naira Biliyan 30 bisa rushe musu shaguna ba bisa ƙa’id ba.

Freedom Radio ta rawaito, a yayin zartar da hukuncin Mai Shari’a Simon Ameboda ya ce bin dare tare da rushe shagunan talakawa haramtaccen aiki ne mai cike da tsantsar zalunci da ƙeta, don haka lallai Gwamnati ta biya masu shagunan.

Haka kuma kotun ta hana Gwamnatin Kano shiga cikin filayen da yin tasirifi da shagunan balle bayar da su ga wani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button