Labarai

Sadaukarwar da ƴan Najeriya sukayi ba za ta tashi a banza ba, zamu tabbatar kowa ya tsaya da kafarsa – Shettima

ya nanata cewa gwamnatinsu za ta cika alkawurran da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa 'yan kasar.

 

Mataimakin shugaban Najeriya ya bai wa al’ummar kasar tabbacin cewa sadaukarwar da suke yi, ba za ta taba tashi a banza ba, ya nanata cewa gwamnatinsu za ta cika alkawurran da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa ‘yan kasar.

Ya ce Shugaba Tinubu ya dukufa wajen gina Nijeriya, inda kowanne dan kasa ke da tabbacin tsayawa da kafarsa ta fuskar tattalin arziki, kuma inda babu wani dan kasar da zai dogara da kudin sadaka wajen gudanar da rayuwa.

Wata sanarwa da Sanata Kashim Shettima ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ta ambato cewa mataimakin shugaban kasar ya yi wadannan kalamai ne ranar Alhamis yayin gabatar da makala a wani bangare na bikin cikar Najeriya shekara 63 da samun ‘yancin kai.

“Yau, mun hadu a nan don karrama kokarin sake fasalin makomar Najeriya. A yau, mun kasance a kan wani matsayin tarihi mai hatsari don yin tsokaci a kan kasar da ta bijirewa hasashen masu mugun fata, ga wannan kasa da ta kasance sha-lugude.

“A tsawon sama da shekara 63, ba kawai mun iya samun bunkasa ba ne saboda kudurin dukkaninmu, himmarmu ta samun ci gaba da juriya a kan akidar hadin kai da ke tabbatar da zamanmu wuri daya daga Aba har zuwa Ogbomosho a dangana zuwa Zariya, duk da kulle-kullen wasu tsiraru,” in ji Shettima.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button