January 19, 2022

Kotu Ta Tabbatar Shugabannin Jam’iyyar APC Na Bangaren Shekarau.

Page Visited: 271
0 0
Read Time:32 Second

Daga Suleman Ibrahim Moddibo

Rahotanni da ke shigo mana na cewa cata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam’iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da aka yiwa Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar APC na jihar da ma dukkan shugabannin da bangaren Ganduje ya gudanar.

Kazalika kotun ta ce bangaren shugabannin da aka zaba a bangaren Sanata Malam Ibrahim Shekarau su ne halastattun shugabannin APC na jihar.

Kotun ta ce bangaren Shekarau, wanda ya zabi shugabanni 17,908, shi ne na hakika.

Banagren Shekarau ya zabi Alhaji Haruna Ahmadu Danzago a matsayin shugaban APC na jihar Kano.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *