January 31, 2023

Kotu Ta Umarci ASUU Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Ke Yi Tsawon Watanni 7.

Page Visited: 1205
0 0
Read Time:54 Second

Kotun ma’aikata ta sawa kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU birki kan yajin aikin da ta ke yi tsawon watanni.

Da yake gabatar da hukunci kan bukatar wucin gadi da gwamnatin tarayya ta nema, Mai shari’ah Polycarp Hamman ya hana kungiyar ASUU ci gaba da yajin aiki har zuwa lokacin yanke hukunci kan shari’ar.

Mai shari’ah Polycap Hamman, wanda alkali ne da ke sauraron shari’ah a lokacin da kotun ke hutu ya kuma mayar da karar zuwa ga shugaban kotun ma’aikata don ya sake bai wa wani alkali wannan shari’ah.

Ma’aikatar kwadago ta kasar ta ce gwamnati ta dauki mataki ne bayan tattaunawa da kungiyar malaman jami’o’in ta ci tura.

ASUU: Dan Me Za A Ce Shugaban Kasa Ya Yi Watsi Da Ilimi? – Garba Doya.

Zamu Rufe Tashoshin Jirgin Sama Dana Ƙasa Da Titunan Idan Ba’a Janye Yajin Aikin ASUU – Ɗalibai.

BBC Hausa ta rawaito cewa, a zamanta na farko, kotun karkashin jagorancin mai shari’a, Polycarp Hamman ta dage sauraren karar zuwa yau Laraba bayan ta saurari bayanai daga wurin masu shigar da kara da wadanda aka shigar kara.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *