June 27, 2022

Kotu tayi fatali da kara kan dakatarda Isa Kudan daga takarar Gwamna a jihar Kaduna.

Page Visited: 187
0 0
Read Time:48 Second

Daga Mu’azu Abubakar Albarkawa.

Babbar kotun Jihar Kaduna da ke zaman ta a Dogarawa ta yi watsi da ƙarar da aka shigar kan ingancin takardun ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP Hon Isah Ashiru Kudan.

Da yake gabatar da hukumcin a zaman da kotun ta yi a Litinin 9 ga watan Mayu,mai Shari’ah Kabir Dabo ya ce masu shigar da karar sun gaza gabatar da gamsassun hujjojin da suka gamsar da kotun kan abubuwan da ake zargin wanda ake kara kan su.

Kotun ta kuma umarci mai shigar da karar ya biya naira miliyan 1 ga wanda ake karar saboda ɓata masa lokaci da kuma rubuta ban hakuri a jaridar daily trust nan da kwanaki 2 masu zuwa.

Da yake karin bayani kan hukuncin kotun,lauyan da yake kare wanda ake ƙara Barrister Zachious Zigwe Adamu ya nuna gamsuwa da hukumcin kuma ya gode ma kotun Saboda tabbatar da abun da yake adalci ga wanda ake ƙara.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *