Kotu Tsare Matashi Watanni 20 Tare Da Biyan Diyya Dubu  50, Bayan Ta Same Shi Da Laifin Saran Wani.

Page Visited: 462
0 0
Read Time:1 Minute, 27 Second

Daga Fa’izu Muhammad Magaji

Wata kotun shari’ar Muslunci mai lamba 2 a jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya, ta tsare wani matashi watanni 20 a Kurkuku, kutun tayi hukuncin ne bayan samun wanda ake zargin da laifin saran wani da Adda.

Kutun ta kuma samu wanda ake zargin mai suna Haidar Abdullahi, Da wani Usman Kakka, da laifin haɗin baki da wajen aikata laifi, da kuma saran wani matashi.

Lamarin ya dai faru ne a ranar 4 ga watan Satumba na wannan shekara ta 2022 da misalin ƙarfe 9 na dare, wanda ake zargin ya gayyato wasu matasa mazauna unguwar Wuntin Dada, suka tare wani mai suna  Mohammed Sani Ibrahim, a cikin unguwar ta Wunti Dada, suka farmasa da makamai irin su wuƙa da adda suka jimasa munanan raunuka a bayansa, a cewar ɗan sanda mai gabatar da ƙara  Rabiu Ibrahim Sarki.

Wanda a yanzu haka matashin ke can kwance a gadon asibiti inda ke karɓar kulawar likitoci.

Aikata laifin da matashin ya yi ya saɓa wa kundin laifuffuka sashi na 125, da 217 na  jihar Bauchi..

Amsa laifinsa da Haidar Abdullahi, ya yi ne yasa kotun yanke masa hukumci.

Kotu Ta Aike Da Matashi Gidan Yari Saboda Satar Goyon Masara 22.

Kotu Ta Tasa Ƙeyar Ɗan Chinan Da Ya Kashe Ummita Gidan Kaso.

Kotu Ta Umarci ASUU Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Ke Yi Tsawon Watanni 7.

Alkalin kotun shari’a musulimci Barrister Muktar Adamu Bello Dambam, ya yanke ma Haidar hukumcin ɗaurin watanni 20 a gidan gyaran Hali, ko kuma zaɓin biyan tara Naira dubu 15, tare da bulala 15, a gaban kotun.

Wakilinmu Fa’izu Muhammad Magaji ya rawaito cewa Haidar zai biya kuɗin diyar jinin da ya zubar wa Mohammad Sani Ibrahim Naira dubu 50.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Matashi Ya Yiwa Mahaifin Budurwarsa Mummunan Rauni Bayan Ya Hana Shi Kaiwa Dare Idan Yaje Zance.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Saurayin ya yiwa mahaifin budurwarsa rauni ne bayan da baban budurwar tasa ya hana shi kaiwa dare idan yaje zance a garin Ɗan Hassan, da ke ƙaramar hukumar Kura ta jihar Kano da ke arewacin Najeriya. Arewa Radio ta rawaito cewa, an jiwa mahaifin budurwar raunine bayan da ya umarce saurayin […]

Read More
Labarai

Sojoji sun sake yin juyin mulki a kasar Burkina Faso.

Sojoji a Burkina Faso sun hamɓarar da shugaban gwamnatin sojan ƙasar, Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba a yau Juma’a, bayan ya hau mulki a watan Janairun da ya gabata. Wata sanarwa da sojojin suka karanta ta kafar talabijin ɗin ƙasar ta ce an rufe dukkan iyakokin ƙasar na ƙasa daga daren yau. Haka nan sun […]

Read More
Labarai

Lauyan Gwamnatin Kano Ya Nemi Kotu Ta Yiwa Abduljabbar Hukunci.

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci dake Kofar Kudu Karkashin me Shari’a Ibrahim Sarki Yola ta ce za ta ayyana ranar da za ta yanke hukunci kan karar da Gwamnatin Jahar Kano ta shigar da Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara bisa zarginsa da kalaman batanci. Yayin zaman na Yau dukkannin bangarorin Shari’ar sun gabatar da Jawabansu na karshe […]

Read More