Daga Firdausi Ibrahim Bakondi
Kotun daukaka kara da ke birnin Abuja ta soke zaben gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara.
Idan za’a iya tunawa a ranar 18 ga watan maris ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana Lawal a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar ta Zamfara.
Sai dai kuma jam’iyyar APC ta kalubalanci nasarar Lawal, wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar PDP a gaban kotu sauraren kararrakin zaɓe a jihar, inda kotun ta amince da zaben Lawal, amma jam’iyar APC ta garzaya kotun ɗaukaka ƙara.
A ranar alhamis din da ta gabata ne kwamitin alkalai uku ya soke nasarar Lawal tare da bayar da umarnin sake gudanar da zaben a kananan hukumomi uku.
Daily Trust ta rawaito cewa, ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Maradun, Birnin Magaji da kuma Bukuyun.