June 27, 2022

Kungiyar likitoti ta tsunduma yajin aiki a Najeriya

Page Visited: 275
0 0
Read Time:56 Second

 

Kungiyar likitoti ta kasar ta tsunduma yajin aiki dukkuwa da kiraye kirayen danda gwamnatin tarayya tayi na dakatar dasu daga yajin aikin.

Da yake jawabi ta kafar talbijin na kasa a safiyar yau, shugaban Kungiyar na kasa Uyilawa Okhuaihesuyi, yace yajin aikin ya fara ne daga karfe 8 na safiyar yau Alhamis.

Ya bukaci gwamnati data dauki matakin daya dace, yana mai cewa matakin tsunduma yajin aikin zai taimaka wa illahirin jami’an kiwon lafiya a fadin kasa baki daya.

Likitotin dai suna neman gwamnati ta gaggauta biyan dukkannin albashi da suke bi tare da kara musu albashi izuwa kashi 50 da kuma biyan alawus na hatsarin covid-19 musamman wa jami’an kiwon lafiya dake manyan asibitoti mallakan jihohi.

Hakazalika sunyi kira kan soke biyan kudin haraji da mambobin Kungiyar ke biya yayin da aka turasu samun horo a wasu cibiyoyi horarda jami’an a fadin kasar nan.

Ministan kwadago da samarda aikin yi Chris Ngige ya roke su dasu gakatar da yajin aikin, don acewar sa rashin likitotin zai kara jefa harkar kiwon cikin tsaka mai wuya, wanda tuni take fama da matsaloli sakamakon annobar covid-19.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *