Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Kungiyar mawakan Firkatul Sahwa da aka yada jita-jita kan mutuwarsu shekaru 13 da suka gabata za su gana da `yan Najeriya a wata ziyarar yabon Annabi da suke yi a jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin kasar.
Sahwa, za su gabatar da majalisin yabon Annabi Muhammad S A W, ne a ranar Asabar da karfe goma na safe a filin wasa na Sani Abacha da ke jihar kamar yadda shugaban Darkikar Kadiriya na Afrika Sheikh Abdulkadir Karibullahi, ta bakin Farfesa Matabuli Kabara, ya ce taron zai samu halartar gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduja da Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da kuma wasu manyan baki.
Mawakan Sahwa Ƴan Ƙasar Sudan Da Aka Yaɗa Mutuwarsu Sama Da Shekaru 10 Suna Nan A Raye.
Ko a ranar Litinin sai da mawakan suka gabatar da majalisin yabon Annabi S A W a gidan Kadiriya da ke jihar Kano a Najeriya.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Har yanzu ina matuƙar son Buhari, in ji fasinjan da ya kuɓuta daga hannun ƴan bindiga.
-
Hana Acaɓa A Jihar Bauchi: Abubawan Da Ake Musu Gaskiya Ba Da Hannun Gwamnatin jihar Bauchi Bane, -Gwanma Bala.
-
KAROTA Ta Kama Wani Matashi Da Ke Sojan Gona Da Sunanta.
-
Gwamnatin Kano Ta Yiwa Sheikh Qaribullahi Kabara Kyautar Fili.
-
Mawakan Sahwa Ƴan Ƙasar Sudan Da Aka Yaɗa Mutuwarsu Sama Da Shekaru 10 Suna Nan A Raye.