Deprecated: Unparenthesized `a ? b : c ? d : e` is deprecated. Use either `(a ? b : c) ? d : e` or `a ? b : (c ? d : e)` in /home/martabaf/public_html/wp-content/plugins/wp-socializer/core/templates/floating-sharebar.php on line 180
Kungiyar NUBASS Ta Yabawa Injiniya Noah Dallaji Kan Shirinsa na Zakulo Yara Masu Baiwa A Nahiyar Afirka - Martaba FM
October 20, 2021

Kungiyar NUBASS Ta Yabawa Injiniya Noah Dallaji Kan Shirinsa na Zakulo Yara Masu Baiwa A Nahiyar Afirka

Page Visited: 139
1 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:1 Minute, 35 Second

 

Shelkwatar kungiyar dalibai ‘yan asalin jihar Bauchi ta kasa NUBASS ta bayyana shirin gidauniyar zakulo yara masu baiwa a nahiyar Afirka da aka kammala a jihar Bauchi a matsayin ci gaba mai ma’ana ba wa zalla jihar Bauchi ba, harma da kasa baki daya.

Shugaban kungiyar dalibai ‘yan asalin jihar Bauchi a matakin kasa da kasa Kwamared Abdulrahman Shu’aibu ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da kungiyar ta kira a Bauchi.

Kwamared Shu’aibu a madadin daliban jihar Bauchi sama da miliyan biyu ya yabawa wanda ya kirkiro shirin Kuma mamallakin Gidauniyar zakulo yara masu baiwa a nahiyar Afirka Injiniya Noah Dallaji bisa kawo shirin jiharsa ta Bauchi, wanda hakan ke alamta cewa shi dan kasa ne na gari mai kishin jihar Bauchi.

Ya kara da cewa makasudin shirin shine zakulo yara masu baiwa, da samar da yanayi mai kyau hadi da tallafa musu, inda ya kara da cewa fadada aikin zuwa Bauchi ci gaba ne mai ma’ana.

Shugaban kungiyar NUBASS ya bayyana shirin wanda shine irinsa na farko a matsayin gagarumin aiki wanda zai ci gaba da zama a zukatan daliban jihar Bauchi musamman wadanda suka ci gajiyar kyautan kudade da Kuma shawarwari kan harkar kwallon kafa.

Kungiyar tace mamallakin Gidauniyar zakulo yara masu baiwa a nahiyar Afirka Injiniya Noah Dallaji ya zama wani allon kwaikwayo da ke karfafa gwiwar yara wajen fito da baiwar da Allah ya yi musu.

Kwamared Abdulrahman Shu’aibu ya yi amfani da damar a madadin daukacin daliban jihar Bauchi wajen yabawa kokarin Noah Dallaji bisa yunkurin shirya zantawa da daliban jihar Bauchi don bayyana musu damammakin tallafin karatu da gidauniyarsa ke samarwa.

Da take tayashi murna bisa nasarar kammala shirin zakulo yara masu baiwar kwallon kafa, uwar kungiyar dalibai a jihar Bauchi tayi kira ga Noah Dallaji da yaci gaba da ayyukan da zasu ciyar da yara gaba a jihar Bauchi, kasa Najeriya da ma daukacin nahiyar Afirka.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us