January 31, 2023

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Kungiyoyin Ɗalibai Ne Kaɗai Za Su Kawo Ƙarshen Lalacewar Makarantu a Jihar Kano -Atiku Kurawa.

Page Visited: 801
0 0
Read Time:1 Minute, 48 Second

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

An yi kira ga kungiyoyin tsofaffin dalibai a jihar Kano da su sanya hannu wajen ragewa gwamnati aiki, domin kawo sauyi mai kyau ga makarantu a jihar.

Malam Ahmad Atiku Kurawa, babban jami’i mai kula da makarantun sakandare na ƙaramar hukumar Dawakin Kudu da ke jihar Kano ne ya yi wannan kiran, yayin wani taron tsofaffin dalibai a jihar.

“To a gaskiya maganar zancen lalacewar makarantu abin ya yiwa gwamnati yawa, magana ta gaskiya kenan, kuma ya kai mutuƙa yadda ba sai lallai ita ce zata yi ba, kuma ba sai lallai ƴan unguwa ba, tsofaffin daliban nan da muke da su, su kaɗai sun isa su riƙe makarantar da suka gama su taimakawa gwamnati a wannan harka,” in ji Atiku Kurawa.

“Aƙalla inma ba za su yi gini ba, daman ba zancen gini ba, to amma a zo a gyara yanayin yadda karatun yake kasancewa ta hanyar taimakawa da kayyakin aiki.”

“Sannan kuma muna bukatar ƙarin ma’aikata su waɗannan tsofaffin dalibai za su iya karɓar kula da masu gadi su dinga biyan su,”inji shi.

Wasu Daga Cikin Makarantun Da Muka Rufe Ba Su Da Mazauni Na Dindindin, -Gwamnatin Kano.

Gwamnatin Ganduje Ta Haramta Zirga-Zirgar Babura Masu Kafa Uku Cikin Dare.

Sarkin Kano Ya Naɗa Kalifan Muhammadu Sunusi Na Ɗaya.

Bashin Da Ake Bin Gwamnatin Kano Ya Jawo Ɗaliban Jihar 15,000 Ba Za Su Rubuta NECO Ba.

Abba Bala Ibrahim, shine wakilin tsofaffin dalibai na makarantar koyon harshen larabci ta Yalwa da ke karamar hukumar Dala a jihar Kano waɗanda suka gama a shekarar 2013.

Ya bayyana farin ciki da jin daɗinsa da yadda ƴan uwansa dalibai suka karɓi taron ta hanyar amsa kira, sannan yace kungiyar za ta yi ƙoƙari wajen kawo sauyi a makarantar da suka kammala.

Abba Bala ya kuma ce za su yi duk mai yiwuwa wajen kawar da mummunar dabi’ar shaye-shaye da faɗan daba a jihar Kano ta hanyar wayar da kan al’umma da bin dukkan wani mataki da zai taimaka.

Taron dai ya samu halartar wasu daga cikin malaman makaranta na lokacin da suka kammala, dama wasu da suke aiki a makarantar a wannan lokaci.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *