Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Jarumin wasan barkwancin Kamal Aboki ya rasu ne a ranar Litiinin sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi a hanar Maiduguri zuwa Kano kamar yadda rahotanni suka ambato.
Tini dai aka yi jana`izar sa a safiyar ranar Talata, kamar yadda addinin musulunci ya tanada, wadda ta samu halartar da dama ciki har da `yan wasan kwaikwayo sanannu a Arewacin Najeriya.
Rasuwar tasa ta girgiza da dama ciki har da abokan sana`ar sa, kasancewar rasuwar ta yi zuwan ba zata.
Falalu A Dorayi, darakta ne a masana`antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ya wallafa sakon ta`aziyyar sa a shafin sa na Facebook “Allah ya jikan Kamal A Aboki Allah ya yi masa gafara ya bawa iyayensa hakurin rashin sa.
”Wani abokinsa kuma makusancin sa wato Kasim Lawan, wanda kuma tare suka fara wasan barkwanci, ya shaidawa Premir Radio, cewa rashin abokin nasa babban gibi ne a rayuwar sa.
Bashir ahmad mai tallafawa shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari kan sadawar zamani ya wallafa a shafin sa na Facebook cewa “gaskiya marigayi Kamal Aboki ya yi zaman amana da samun sheda mai kyau daga gun yan uwa a musamman abokan aikin sa, Allah ya jikansa, ya gafarta masa, yasa Aljanna ce makomar sa.
”Kin Indara, wani mai amfani da Soshiyal Midiya ne shima ya yi masa addu`a “ubangiji Allah ka yi masa rahma, kasa Aljanna makoma.”
Suma mabiya shafin Martaba FM ba a barsu a baya ba inda a comments dinsu ma banbanta suka dinga yi masa addu`o`in samun rahama da gafarar Allah.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Jarumin Ya Rasu Ne Bayan Ya Yi Fama Da Rashin Lafiya.
-
Hadarin Kwale-kwale Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 24 A Bangladesh.
-
Sarkin Jama’are Muhammad Wabi Ya Rasu Bayan Shafe Shekaru 50 Bisa Mulki.
-
Cikin Kwanaki Biyar Kano Ta Rasa Jigaganta Biyu.
-
Marigayi Alhaji Bashir Othman Tofa: Abinda Na Sani Game Da Rayuwarsa.