January 19, 2022

Ma’aikatan Jinya Za Su Janye Daga Asibitocin Gwamnatin Jihar Bauchi.

Page Visited: 369
0 0
Read Time:1 Minute, 14 Second

Daga Suleman Ibrahim Moddibo

Ƙungiyar ma’aikatan jinya na sa kai a jihar Bauchi mai mambobi 2897 sun yi barazanar janyewa daga asibitoci sakamakon wasu alkawura da suka ce gwamnati ta gaza cika musu.

Makwannin da suka gabata ne dai kungiyar ta ba da wa`adin makwanni biyu domin gwamnatin jihar Bauchi ta nema musu mafita ko ta janye daga ayyukan da suke yi na sa kai a nan jihar.

Buƙatun da suke neman gwamnatin jihar Bauchi ta biya musu sune “a ɗauki mambobin kungiyar aiki na dindindin ko kuma a dunka biyan wasu kuɗaɗe da za su dunga rage buƙatu a duk wata” in ji Shugaban kungiyar Yusuf Abdullahi Fada.

Fada ya ce, kwanaki 14 bayan ba da wa`adin har yanzu kungiyar tace shiru babu wanda ya tuntubeta “adon haka haka zamu janye ma’aikatanmu”.

Wakilinmu a jihar Bauchi ya tuntubui kwamishinan lafiya na jihar Bauchi Dr. Sama`ila Dahuwa Kaila shin ko gwamnati tasan da wannan koke nasu kuma me suke yi a kai?

Dr. kaila sai ya ce, “gwamnati tana iya kokarinta dan taga cewa tayi maganin waɗannan al’amuran mu fahimci cewar gwamnati tana da bukatar ma’aikata kuma ma tafi su san ta ɗauke su, to amma yanayi ne na kuɗi da abubuwa wanda suka zo suka kawowa gwamnati wani tarnaki”.

Ya kuma ce zuwa yanzu an cimma narasa domin nan gaba kadan za su kawo karshen matsalolin, to amma ya ce tsaikon da aka samu ya biyo bayan wasu matsaloli ne da aka fuskanta.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *