December 2, 2021

Mai Yasa Gwamnan Jihar Bauchi Ya Dakatar Da Shugabar Hukumar Kula Da Marayu Da Marasa Galihu Hassana Arkila?

Page Visited: 146
0 0
Read Time:30 Second

Daga Suleman Ibrahim Moddibo

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad Abdulkadir ya amince da dakatar da shugabar Hukumar Kula Da Marayu Da Marasa Galihu ta jihar Bauchi Hassan Arkila Tawus.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai baiwa gwamnan jihar Bauchi shawara kan yada labarai Mukhtar Gidado da ya aikewa manema labarai.

Meye Dalilin Dakatar Da Ita?

Acewar sanarwar, an dakatar da ita ne don bada damar yin bincike kan zargin aikata ba daidai ba.

Sanarwar ta unarce ta da ta mika dukkanin ayyukan hukumar ga jami’i mafi girma a hukumar har sai an kammala bincike.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *