Deprecated: Unparenthesized `a ? b : c ? d : e` is deprecated. Use either `(a ? b : c) ? d : e` or `a ? b : (c ? d : e)` in /home/martabaf/public_html/wp-content/plugins/wp-socializer/core/templates/floating-sharebar.php on line 180
Majalisar Zartaswar Jahar Katsina Ta Amince Duk Matashin Da Yakai Shekaru 18 Zai Dunga Biyan Hrajin Naira 2000. - Martaba FM
October 20, 2021

Majalisar Zartaswar Jahar Katsina Ta Amince Duk Matashin Da Yakai Shekaru 18 Zai Dunga Biyan Hrajin Naira 2000.

Page Visited: 115
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:1 Minute, 3 Second

Gwamnatin iahar Katsina ta amince kowanne mazaunin jihar , da ya kai shekara 18 zai dunga biyan harajin naira dubu 2000 a duk shekara.

Kwamishinan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki na Jihar, Faruq Lawal Jobe ne ya bayyana haka a ranar Laraba bayan kammala taron majalisar Zartaswar jahar.

Joɓe ya bayyana cewa haraji ya shafi ma’aikacin gwamnati da wanda ba ma’aikacin gwamnati ba, mai Sana’a da ma wanda baya sana’ ar, ɗan jiha da ba ɗan jaha ba duka ya wajaba a kan kowa.

Sai dai Mata an ce mai aikin albashi, ita ce kadai za ta biya harajin.

Harajin dai wanda aka kira da “harajin raya kasa” kwamishinan ya ce an tsara yadda za’a dunga karbarsa inda ya ce sun bullo da wani tsari da zai dauki bayanan yawan dukiya da hoto da katin kuri`a ko katin zama dan Kasa da lambar BVN da kuma wadanda ke makwabtaka da wanda ya biya harajin.

A ɓangaren jangali kuma Jobe ya ce duk wanda ya mallaki shanuwa zai biya naira dari biyar a kan kowane sa ko shanuwa a duk shekara.

Jihar Katsina dai na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalar hare-haren `yan fashin daji masu garkuwa gami barayin shanu.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us