Makarantun Wuni Na Mata-Zalla A Jahar Bauchi Za Su Fara Ran 25 Ga Satumba

Page Visited: 202
0 0
Read Time:1 Minute, 54 Second

Majalisar Zartarwa ta Jahar Bauchi (Bauchi State Executive Council) a zaman da ta yi jiya, 9 Satumba, 2022, wanda Gomna Bala Abdulkadir Mohammed ya shugabanta, ta sahhale wa Ma’aikatar Ilimi fito da tsarin da zai hana cakudewar dalibai maza da mata a makarantun sakandaren wuni a Jahar, duk inda haka, ko lokacin da haka, zai yiwu.

A cikin takardar bukatar sahhalewar (memo), Ma’aikatar Ilimin ta nuna bukatar fadada umarnin da gomnatin soja ta Jahar ta bayar a 1978 wanda ya hana cakuda maza da mata a makarantun sakandare wadanda suke dukkanninsu na kwana ne a lokacin.

Ma’aikatar ta nuna cewa fadada hanin zuwa makarantun wuni da aka kirkiro daga baya zai taimaka wajen kiyaye gagarumin cigaban da aka samu a ilmin yara mata a Jahar, da kuma kara yawan yan’matan da iyaye za su bari su wuce makarantun firamare har zuwa babbar sakandare, da sauwake gudanar da makarantun, da kyautata tarbiyar daliban, da hana yaduwar bad’ala tsakaninsu wanda yaduwar kafofin sadarwa na zamani ke haddasawa.

Kafin mika bukatar sahhalewar, Jami’an Ma’aikatar Ilimi sun ziyarci Sarakuna da masu ruwa-da-tsaki a fannin ilimi na Jahar a garuruwan Ningi, Jama’are, Azare, da Misau, bayan tuntubar shugabannin makarantu da PTA/SBMC a Bauchi don karbar nasu shawarwarin game da wannan tsarin wanda kowa ya yi amanna da shi. Yau ja’mi’an za su ziyarci Masu Martaba, Sarakunan Bauchi da Dass don yi musu albishir na aiwatar da wannan tsari.

Da yardar Allah, tsarin na mata-zalla a makarantun sakandare an kudiri fara shi ran 25 ga wannan watan lokacin da dalibai za su fara sabuwar shekarar karatu, musamman a manyan garuruwar Jahar. Ma’aikatar ilimi ta kamala duk shirye-shiryen aiwatar da shirin wanda zai zo a mataki-mataki gwargwadon halin da makarantun suke da kuma samuwarsu a cikin garuruwan Jahar. Akwai sanarwa (circular) wacce Ma’aikatar Ililmi za ta fitar a game da yanda aiwatar da tsarin zai kasance.

A cikin sati mai zuwa, Ma’aikatar Ilimi za ta fitar da jadawali (list) wanda a ciki duk daliban da abin ya shafa za su san wadanne makarantu za su koma, in sha Allahu.

Da fatar al’umma za su taya Gomnati da addu’a na samun nasarar shirin.

Dr. Aliyu U. Tilde
Komishinan Ilimi

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ilimi

Ta Leƙo Ta Koma: Gwamnatin Najeriya Ta Janye Umarnin Da Ta Bayar Na Buɗe Jami’o’i.Q

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Gwamnatin tarayya ta janye umarnin da ta ba shuganannin jami’o’i na su koma bakin aiki. Tinda farko a safiyar ranar Litinin ɗin nan gwamnatin ta bawa shugabannin jami’o’in umarnin buɗe makaratun cikin wata wasiƙa mai lamba NUC/ES/138/Vol.64/135 da kungiyar NUC ta fitar. To sai dai ta yammacin ranar wata wasiƙar ta […]

Read More
Ilimi

Gwamnatin Najeriya Ta Umarci Shugabannin Jami’o’i Su Buɗe Makarantu.

Gwamnatin tarayya ta umarci shugabannin jami’o’i (VCs) da su sake bude makarantu tare da baiwa dalibai damar komawa karatu. Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun daraktan kudi da asusun kula da jami’o’in kasar, NUC, Sam Onazi, a madadin babban sakataren hukumar, Farfesa Abubakar Rasheed a Abuja a yau […]

Read More
Ilimi

Kotu Ta Umarci ASUU Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Ke Yi Tsawon Watanni 7.

Kotun ma’aikata ta sawa kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU birki kan yajin aikin da ta ke yi tsawon watanni. Da yake gabatar da hukunci kan bukatar wucin gadi da gwamnatin tarayya ta nema, Mai shari’ah Polycarp Hamman ya hana kungiyar ASUU ci gaba da yajin aiki har zuwa lokacin yanke hukunci kan shari’ar. Mai […]

Read More