August 8, 2022

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Masu Gidajen Burodi Sun Janye Yajin Aiki Sun Kuma Yi Ƙarin Kuɗin Burodi.

Page Visited: 786
0 0
Read Time:1 Minute, 21 Second

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Wata Ƙungiyar masu gidajen burodi ta ƙasa rashen jihar Bauchi ta janye yajin yajin aikin da ta shiga tsawon wuni uku, saboda tsadar kayan da ake bukata wajen yin burodin.

Mambobin ƙungiyar ta Master Bakers and Caterers a faɗin ƙasa ne suka shiga yajin aikin tin daga ranar Alhamis har zuwa ranar Asabar.

Shugaban ƙungiyar na jihar Bauchi Adamu Baba Muhammadu Jahun, ya ce sun janye ne saboda halin matsayi da suka ga al’ummar jihar Bauchi sun shiga saboda rashin burodin.

“Duba da halin irin nitsasun da mutane suka shiga muka ga yakamata mu janye yajin aikin nan namu, alabarshi mu ɗan yi wani ƙarin farashi ɗan kaɗan.”

Wanda zuwa yanzu ya ce sun yi ƙarin kaso talatin cikin ɗari ne kawai kafin ganin mai hali zai yi.

“Sai muka ƙara kashi talatin cikin ɗari a kan farashin da muke da shi da, misali akwai wani burodi wanda da ake sai da shi naira ɗari,  to yanzu zai koma ɗari da ashirin ne a kan teburi, akwai wanda kuma ake sai dashi naira ɗari da ashirin zai koma ɗari da hamsin, ro manyan burodi kuma shine duk za a yi masa wannan ƙarin kashi talatin dana ambata maka,” inji Baba Muhammadu.

Tinda fari cikin wata zantawarsa da Martaba FM a birnin Bauchi ya ce zuwa yanzu akwai aƙalli gidajen burodi sama da 40 da suka rufe sanadin tsadar rayuwa.

“Idan aka tafi a haka, to zai zama cewa gidajen burodi da daman gaske za su rufe, yanzu haka ina tabbatar maka a wannan jiha tamu sama da gidaje 40 sun rufe saboda halin da ake ciki tsadar abubawa.”

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *