December 2, 2021

Matar Aure Ta Kashe Mijinta Saboda Ya Nemi Biyan Bukatar Aure.

Page Visited: 955
0 0
Read Time:36 Second

Rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta kama wata matar aure mai shekaru 18 mai suna Salma Hassan, da ke karamar hukumar Itas Gadau ta jihar Bauchi, bisa zargin kashe mijinta mai suna Mohammed Mustapha da wuka.

Salma, yayin da ta shiga hannun ‘yan sandan a hedkwataersu da ke Bauchi, babban birnin jihar a ranar Alhamis, ta ce “Ban so kashe mijina ba, tsautsayi ne. Na soka mishi wuka a kirji ne saboda ya takura ni dole sai ya kwanta dani. Na zata iskanci ne jima’i, shiyasa na ki amince wa.

“Na yi dana-sanin kashe mijina. Na so amfani da wukar ne don tsorata shi. Ban san cewa hakan za ta faru ba,” kamar yadda ta bayyana a ofishin yan sandan.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

One thought on “Matar Aure Ta Kashe Mijinta Saboda Ya Nemi Biyan Bukatar Aure.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *