December 2, 2021

Matashin Dan Najeriya Ya Kirkiri Manhajar Sada Zumunta.

Page Visited: 131
0 0
Read Time:51 Second

Wani haziƙin matashi masanin na’ura mai kwakwalwa dan asalin ƙaramar Hukumar Kirfi dake jihar Bauchi, mai suna Abdullahi Yahaya, shine ya kirkiri wannan sabuwar manhaja wacce take cike abubuwa masu saukin gaske musamman ga ma’abota rubuce-rubuce a kafafen sadarwa na zamani.

Manhajar dai wacce aka yi mata suna da “Tabarau” tana kunshe da dukkanin abubuwan da sauran kafafen sadarwa suke dauke da shi kamar Facebook, Twitter, Instagram da dai sauransu.

Hakazalika dai-daikun mutane, masana’antu, makarantu dama gidajen ta hanyar kirkiran shafi da kuma gabatar da shirye-shirye kai-tsaye musamman wanda ake da bukatar gudanar dasu yadda jama’a za su gani ta hanyar hoto mai motsi (Video) duk dai a cikin wannan fitacciyar manhaja ta “Tabarau”.

A yanzu dai dumbin mutane daga sassa daban-daban na ciki da wajen ƙasar nan ke cigaba da yin rijista da wannan manhaja domin cigaba da gudanar da harkokinsu na rubuce-rubuce a kafafen sadarwa.

Kuma yanzu haka Manhajar na nan a Play Store domin saukewa.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *