December 2, 2021

Matsalar Rashin Tsaro Da Tsadar Rayuwa Sun Dami Al’ummar Najeriya – Kabara.

Page Visited: 788
0 0
Read Time:57 Second

Daga Suleman Ibrahim Moddibo

Anyi kira ga shugaban ƙasar Najeriya Muhammad Buhari, da jami’an tsaro su yi duk mai yiwuwa wanjen tabbatar da tsaro da kuma magance tsadar rayuwa da ake fama da su Najeriya.

Shugaban ɗarikar Ƙadiriyya na Afrika Sheikh Abdulƙadir Ƙariballahi Sheikh Muhammad Nasiru Kabara, ne yayi wannan kiran yayin da yake jawabi a wajen taron murnar haifuwar shugaban ɗarikar Ƙadiriyya na duniya baki ɗaya Sheikh Abdulƙadir Jilany karo na 71 da ya gudana a jihar Kano.

Sheikh Ƙaribullahi ya ce, akwai matsaloli guda biyu da suke damun Najeriya, na farko shine matsalar tsaro da aminci da zaman lafiya, “muna kira ga mai girma shugaban kasa tare da jami’an tsaro su dada tsayawa aga cewa an kawo karshen matsalar rashin tsaro a sauran guraren da suka rage a Najeriya”.

Ya ce, abu na biyu da ake fama dashi yanzu a Najeriya shine hauhawar farashin abinci da tsadar rayuwa wanƴan nan al’amura sun dami al’ummar Najeriya, “hauhawar farashi da tsadar rayuwa kullum Nairan mu tana tafiya tana kara yin kasa to muddin wannan tana nan zamu cigaba da samun kanmu cikin damuwa da tsananin rayuwa da rashin kyakkyawan aminci”.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *