September 22, 2021

Matsalolin Da Suka Dabaibaye Bangaren Ilimi A Najeriya Suna Da Yawa.

Page Visited: 105
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:1 Minute, 57 Second

Daga Suleman Ibrahim Moddibo

Batun faduwar yara NECO a jihar Kano yaja hankalin marubuta a shafukan sada zumunta sun ta fito da bayanai da kiraye-kirayen sauya salon inganta ilimi.

Gaskiya girman matsalar rashin kyawun yanayi ga harkar ilimi a kasar nan yakai inda yakai musamman ga wanda abun ya shafa ko yake zagawa irin wadannan makarantu yake ganewa idonsa yadda  abun yake yasan akwai babbar matsala sosai.

Babbar matsala ta farko ita ce rashin kwararrun malamai.

Rashin kayan aiki tare da tafiya daidai da zamani.

Rashin yanayi mai kyau ga tsarin koyarwar tun daga matakin farko zuwa sama.

Mu dauki na farko shine rashin kwararrun malamai, idan har malami yana da kwarewa da taribiya irin ta koyarwa tare da ilimi sosai a fannin da yake koyarwa to tabbas za a samu ilimi mai kyau ga wanda ake koyarwa koda kuwa a gindin bishiyoyi ake koyarwar, indai har malami yana da kwarewa to za a samu cigaba amma idan har aka sara malami shakka babu an rasa ilimi tinda babu mai koyarwa da kyau.

Abin takaici idan kaje makarantu kaga yadda malamai suke koyarwa a yanzu zaka sha mamaki tare da jin tausayin wadanda ake koyarwar.

Suma malaman da ke koyarwa dole ne suji tsoron Allah idan sun san ba su da kwarewar karma su soma neman aikin koyar dan ba zai yuwa wanda bashi da kwarewa ya dunga koyar da wadanda suke koyo ba.

Alhakin yana wuyan gwamnati ta tabbatar ma’aikatanta suna da kwarewa irin yadda yakamata ba wai yan alfarma ba, ba kuma yan zari zuga ba su musamman ma a kanarantu irin na gwamnati dole ne gwamanti ta canza salo tayi kokari bawa kowanne malami woro na musamman kan koyarwa ta tabbatar ta dauki mutumin da ya dace aiki.

Idan gwamnati zata dauki malami ta tabbatar cewa yana da ra’ayin koyarwar ba wai zai yi aikin ba don ya rasa aikin yi, dan a yanzu dayawa mutane suna koyarwa ne don sun rasa abun yi sai su dunga aikin koyarwa, kuma sam ba haka tsarin ya dace ba.

Lallai gwamnatoci su ji tsoron Allah su tina cewa wata rana za su sauka suyi kokarin yin aiki mai kyau ta yadda za a dunga tinawa da su.

Gwamnati tayi duk me yiwuwa wajen inganta aikin kayarwa domin samun al’umma mai ilimi anan gaba, idan har domin al’umma suke mulkin.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us