September 22, 2021

Mayakan Boko Haram Biyar Sun Hadu Da Aljalinsu A Hannun Sojojin Najeriya.

Page Visited: 113
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:30 Second

Dakarun rundunar musamman a yankin arewa maso gabashin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga 11 tare da ƙwace makamai, a cewar rundunar sojan Najeriya.

Kakakin rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya faɗa ranar Lahadi cewa dakarun na rundunar Operation Hadin Kai sun ƙwace wata mota maƙre da man fetur ta mayaƙan Boko Haram ko kuma ISWAP.

A cewarsa cikin wata sanarwa, sojojin na kan aikin fatro ne a kan hanyar Ngoshe zuwa Ashigashiya a JIhar Borno yayin da suka fafata da mayaƙan ƙungiyar a yankin Daushe.

Bayan fafatawar ce kuma, dakarun suka gano bindigar AK-47 ɗaya da fakitin harsashi ɗaya.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us