January 31, 2023

Mayakan ISWAP sun hallaka jami’an tsaro da farar-hula a Borno.

Page Visited: 92
0 0
Read Time:36 Second

Mayakan jihadi sun kai hari sansanin soji da wani yankin Borno tare da kashe sojoji 9, da ‘yan sanda biyu da kuma farar-hula, kamar yada majiyoyin tsaro da mazauna yanki suka tabbatar.

Mayakan IS sun farwa garin Malam Fatori, a ranakun daren Juma’a da kuma safiyar Asabar, a cewar majiyoyin.

A cewar bayanan da aka fitar, an tafka asara sosai a harin.

Harin na farko, a kusa da iyakar Najeriya da Nijar anyi ɓarin wuta sosai tsakanin sojoji da mayakan, a cewar Buji Garwa.

A watan Maris da ya gabata ne, dubban mutane da rikicin Boko Haram ya tilastawa tserewa zuwa Nijar, suka dawo yankunansu a Malam Fatori.

Mun dauko wannan labarin a shafin kai tsaye na BBC Hausa.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *