June 27, 2022

Mun zamo daya tamkar da dubu – Shugaban asibitin ABUTH Zaria.

Page Visited: 426
1 0
Read Time:2 Minute, 38 Second

Daga: Mu’azu Abubakar Albarkawa, Kaduna.

Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello dake Shika Zariya ta dukufa wajen ganin ta bunkasa kiwon lafiyar al’umma, da zama daya tamkar da dubu wurin gudanar da harkokin ta a matsayin tana daya daga cikin manyan asibitocin kasar nan da gwamanti ke alfahari da ita.

A zantawar shi da Martaba FM a ofishin sa, Shugaban Asibitin Farfesa Hamidu Ahmad Umdagas, ya bayyana cewar tun zaman shi shugaban Asibitin a shekarar data gabata, an samu gagarumar nasara a sha’anin gudanarwar Asibitin da baza’a iya mantawa da su ba.

Acewar shi, Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello Shika Zariya da aka samar tun shekaru da dama da suka wuce, zuwa yanzu hobbasan da akeyi ya zama abin alfahari da tunkaho, ganin yanayin jagorancin da’ake sashi a yanzu haka.

Farfesa Hamidu Ahmad yace wasu daga cikin nasaroron da aka samu a Asibitin sun hada da samar da karin katafaren dakin kula da marasa lafiya na gaggawa wato (Emergency) domin rage cunkoson da ake samu a tsohon da ake dashi.

Har ila yau Kuma, anyi fadi tashin ganin gwamnati ta amince sun dauki ma’aikata da za su maye gurbin wanda suka aje aiki ko suka canza wuraren aiki ko kuma suka rasa rayukan su.
Hakan kuwa na nufin samar da karin ma’aikatan jinya da zasu cigaba da samar da kulawa ga marasa lafiya da suke zuwa Asibitin daga sassan kasar nan.

A bangaren tsaftar muhalli kuwa, a cewar Farfesa Hamidu, tun a tsawon lokaci, an san cewa harabar Asibitin na fama da wari saboda sinadaran da ake amfani da su wurin tafiyar da lamuran yau da kullum, yanzu haka bisa wasu kudade da suka samu daga bangaren gwanati sun dauki ragamar kawar da wannan wari, kuma sun yi nasara da yanzu mahalarta za su iya shiga Asibitin su fita ba tare da sunji wani wari da zai kawo masu cikas wurin tafiyar da harkokin su ba. Kuma a cewar shi farawa ne domin suna da tsare-tsare da ake sa ran zai kara kai Asibitin zuwa ga tudun mun tsira.

Baya ga nan, akwai aikin katafaren gyaran dakunan kwanan majinyata da ofisoshin Ma’aikata,bugu da kari akwai manyan na’urorin kula da marasa lafiya wanda wasu ma babu irin su a fadin kasar nan.

Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello Shika, na da tsawon akalla kilomita Daya da d’igo Uku ne, Wanda a da idan aka shiga musamman da dare, Asibitin na fama da duhu saboda rashin fitillu da zai haska sassan Asibitin, amma yanzu haka a cewar Farfesa Hamidu Umdagas, sun sanya manyan fitillu masu aiki da hasken rana da zasu kara inganta sha’anin tsaro da gudanarwar Asibitin.

Daga nan sai ya gode ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamanan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-rufa’i saboda cikakken hadin kai da goyon baya da suke ba Asibitin domin ta cigaba da rike matsayin ta na babbar Asibitin da al’ummar Arewacin Najeriya suke alfahari da ita.

Kuma ya gode ma daukacin membobi kwamitin gudanarwar Asibitin da masu taimaka masa a fannoni daban-daban da kuma Sarakuna iyayen kasa musamman Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris bisa aikin da suke ba dare ba rana domin ganin cigaban Asibitin.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *