January 31, 2023

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Muna Neman Tabarrukin Ku- Saƙon Gwamna Bala Ga Sarakuna

Page Visited: 70
0 0
Read Time:1 Minute, 45 Second

 

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad yace gwamnatin sa ba za ta gajiya ba wajen tabbar da sabunta jihar ta hanyar cigaba da gudanar da ayyukan raya ƙasa da bunƙasa tattalin arziki don walwalar al’umar ta.

Bala Muhammad ya bayyana haka ne yayin ziyarar neman tabarruki daga iyayen ƙasa, masu martaba sarakunan Bauchi, Dass, Misau, Jama’are da Katagum a fadojin su inda ya shaida musu cewa ya kai ziyarar ne don sanar da su ƙudurin sa na fara gangamin yaƙin neman zaɓe karo na biyu da zai fara gobe Alhamis.

Muhammad yace a matsayin su na iyayen ƙasa kuma shugabanni, sarakuna na taka muhimmiyar rawar tabbatar da ɗorewar zaman lafiya da walwalar al’uma kana yace ya zama wajibi ya nemi izini da tabarrukin su don kai ga nasara.

Gwamna Bala wanda ya samu rakiyar jiga-jigan gwamnatin sa da shugabannin jam’iyyar PDP matakin jiha, yace gwamnatin sa ta bada dama wa ƴan adawa baza hajar kamfe ba tare da hantara ba amma ba za ta lamunci ta-da-zaune-tsaye ko wani abu da ka iya raba kai ko kawo cikas ga haɗin kai da zaman lafiya a dukkanin lunguna da saƙon jihar Bauchi ba.

Yayi kira ga sarakuna da masu riƙe da masarautun gargajiya da su ƙauracewa duk wani abu da ka iya taɓa mutuncin ko masarautun su da sunan siyasa kana ya ƙara da cewa gwamnatin sa za ta cigaba da mara musu baya wajen tabbatar da sauƙe nauyin shugabancin da suka gada iyaye da kakanni.

Yayi amfani da damar wajen yabawa goyon baya da haɗin kai da sarakunan ke bada gwamnatin sa wajen wayar da kan al’uma dangane da ayyukan gwamnati a yankunan su tare da kira a gare su da kada su gajiya wajen gudanar da addu’oin zaman lafiya da cigaba me ɗorewa a jihar Bauchi da ma Najeriya baki ɗaya.

A jawaban su daban daban, masu martaba sarakunan Bauchi, Dass, Misau, Jama’are da Katagum fatan alheri suka yi wa gwamnan tare da yaba masa kan samar da romon dimokraɗiyya ciki har da gyara da kwaskwarima wa fadojin sarakuna, dagatai da hakimai.

 

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *