Mutane 41 Sun Kamu Da Cutar Ƙyandar Biri A Najeriya.

Page Visited: 148
0 0
Read Time:1 Minute, 1 Second

Akalla mutane 41 ne suka kamu da cutar Kyandar biri cikin kwanaki Bakwai a fadin Najeriya.

Hukumar dake dakile cututtuka masu yaduwa NCDC itace ta bayyyana haka a shaifin ta cikin sakon da ta saba fitarwa a Twitter.

NCDC ta ce mutane 41 ne suka kamu da annobar cutar Kyandar biri daga ranar 29 ga watan Augusta zuwa 4 ga watan satumba shekarar da muke ciki.

Sannan cikin jihohin da masu annobar suka fito mafi yawanci daga kudancin kasar ne kuma sun hada da Jihar Legas da 14 sai Abia 7 da kuma Imo 6 Ogun 5 Ondo 2.

Sauran jihohin su ne Akwa Ibom 1 Borno 1 Delta 1 Oyo 1 Plateau 1 Rivers ma mutum 1.

Sannan mutane dake dauke da cutar a halin yanzu sun kai su 318 bayan mutuwar mutane 7 a fadin Najeriya.

NCDC ta ci gaba da bayyyana cewa cutar Kyandar biri cuta ce wadda ke zuwa lokaci ta na kara yaduwa a kasashen Afrika musamman ga yankin talakawa

Sannan Kyandar biri ta hallaka mutane da dama kuma ta fi tasiri akan yara kanana.

Hukumar tace ta na ci gaba da dakile cutur a fadin kasar nan ta yadda za a kawo karshen matsalar a fadin baki ɗaya.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Lafiya

Najeriya Na Shirin Ko Ta Kwana Kan Barazanar Barkewar Cutar Ebola.

Hukumomin Najeriya sun ce kasar na fuskantar barazanar barkewar cutar Ebola, da ake tunanin shigo da ita daga kasar Uganda. Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasar NCDC ta ce an samu karuwar baranazar barkewar cutar ne sakamakon yawan zirga-zirgar fasinjoji da aka yi tsakanin Najeriya da Uganda, da kuma cudanyar fasinjoji, musamman a filayen […]

Read More
Lafiya

INGANTACCIYAR MAGANIN HIV (ƘANJAMAU).

Babbar cibiyar magani na Musulunci wato kashful Aleel, tabbas suna bada maganin Cutar ƙanajamau kuma ana warkewa, wanda akwai shaidu masu yawa da suka tabbatar da wannan cibiyar suna bada maganin HIV Akwai mutane 3 a Sokkoto da suka warke daga wannan cutar dalilin karɓar maganin su, akwai mutum hudu a Kano, akwai mutum ɗaya […]

Read More
Lafiya

ILLOLIN ISTIMNA’I (ZINAR HANNU) TARE DA MAGANIN SA.

Istimna’i shine mutum ya biyawa kansa buƙata ta hanyar wasa da gaban sa, hakan yana haifar da matsaloli masu yawan gaske sannan kuma haramun ne YANA HAIFAR DA MATSALOLI KAMAR HAKA 1 Yana haifar da ƙanƙancewar gaba 2 Rashin haihuwa 3 yana saka yawan mantuwa da rashin riƙe karatu 4 saurin inzali yayin jima’i 5 […]

Read More