Naɗa Ƙasurgumin Ɗan Fashi Sarauta A Zamfara Ya Jawo An Dakatar Da Sarkin Da Ya Yi Naɗin.

Page Visited: 658
0 0
Read Time:1 Minute, 50 Second

Rahotannin daga jihar Zamfara a Arewa maso yammacin Najeriya na cewa gwamnatin jihar ta dakatar da Sarkin ‘Yandoton Daji bayan da ya bai wa wani jagoran ‘yan fashin daji, Adamu Aliero, sarautar Sarkin Fulani.

Gwamnatin ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadin karashen makon daya gabata.

A cewar sanarwar wadda ta samu sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Kabiru Balarabe Sardauna, tun farko gwamnatin ba ta da masaniyar naɗin da aka yi wa Adamu, wanda hukumomi ke nema ruwa-a-jallo.

Sanarwar ta ce a yanzu an mika riƙon sarkin garin na ‘Yandoto ga Alhaji Mahe Garba Marafa, wanda shi ne Hakimin ‘Yandoto.

Haka nan sanarwar ta ce gwamnati ta kafa kwamitin da zai yi bincike kan naɗin sarautar da aka yi wa mutumin da ake kira Ado Aliero.

A ranar Asabar din karshen makon ne dai bayanai suka fito kan yadda Sarkin na ‘Yandoto ya naɗa Adamu Alieru ‘Yankuzo, wanda ake zargin jagoran ‘yan fashin daji ne a matsayin Sarkin Fulani, lamarin da ya janyo suka daga bangarori da dama.

BBC Hausa ta rawato cewar rundunar ‘yan-sandan Najeriya, ta bayar da cigiyar wanda aka naɗa sarautar ne shekaru biyu da suka gabata.

Daga Yanzu Duk Wani Ɗan Zamfara Zai Iya Mallakar Bindiga Domin Ya Kare Kansa.

Ana Fargabar ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mahalarta Biki 50 A Zamfara.

Babu Wani Sarkin Sharifan Najeriya A Jihar Zamfara – Majalisar Sarkin Sharifan Najeriya.

SP Gambo Isa, wanda shi ne mai magana da yawun rundunar ‘yan-sandan Najeriya a jihar Katsina, ya tabbatar wa BBC da batun.

Ya ce “Adamu Aliero na daga cikin masu kashe mutane da kama mutane su yi garkuwa da su, kuma muna nemansa a kan aikin ta’addanci da ya yi a garin Kadisau, inda ya kashe sama da mutum ɗari.”

Ya ƙara da cewa “Mun yi gangami tare da ‘yan-jarida da tsohon Kwamishinan ‘yan-sanda Sunusi Buba, muka je garin Kadisau muka ga kisan-gilla da ya yi wa mutane.”

Wannan ne ya sa rundunar ‘yan-sanda reshen jihar Katsina ta fitar da sanarwar cewar duk wanda ya kawo Adamu Aliero a raye za a ba shi (ladan) Naira miliyan biyar, kuma maganar tana nan.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Tsaro

Mayakan ISWAP sun hallaka jami’an tsaro da farar-hula a Borno.

Mayakan jihadi sun kai hari sansanin soji da wani yankin Borno tare da kashe sojoji 9, da ‘yan sanda biyu da kuma farar-hula, kamar yada majiyoyin tsaro da mazauna yanki suka tabbatar. Mayakan IS sun farwa garin Malam Fatori, a ranakun daren Juma’a da kuma safiyar Asabar, a cewar majiyoyin. A cewar bayanan da aka […]

Read More
Tsaro

Kano: Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Jawo Rasa Ran Mutum Guda Da Jikkata Wasu Biyar – Ƴan Sanda.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Rundunar ƴan sandan jihar Kano da ke Arewa maso yammacin Najeriya, ta tabbatar da mutuwar mutum ɗaya inda kuma biyar suka jikkata sakamakon rikicin Manoma Da Makiyaya da ya afku a garin Kuka Bakwai, da ke ƙaramar hukumar Minjibir a jihar. Rundunar yan sandan ta ce an samu ɓarkewar  rikicin ne […]

Read More
Tsaro

Masu Garkuwa Sun Bukaci A Basu Kudin Fansa Har Naira Miliyan 250 A Katsina Bayan Sun Sace Mutum 43.

Daga Suleman Ibrahim Maddibo wasu bayanai daga jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya na cewa, al’ummar kauyen Bakiyawa da ke yankin Batagarawa na cikin firgici bayan da ‘yan ta’addan da suka sace mazauna kauyen 43 suka bukaci da a biya su naira miliyan 250 a matsayin kudin fansa, kafin sako mutanen da suke […]

Read More