August 8, 2022

Nafi Son Kashe Mutane Maimakon Garkuwa Da Su, -Ado Alero.

Page Visited: 3882
1 0
Read Time:1 Minute, 9 Second

Daga Suleman Ibrahim Modibbo.

Shahararren ɗan bindigar nan ya addabi jihar Zamfara da Katsina da wasu sassan Arewa maso Yammacin Najeriya Ado Alero Ƴandoto wanda kuma aka naɗa sabon Sarkin Fulanin Ƴandoton jihar Zamfara ya ce ba shi da burin yin garkuwa da mutane amma ya fi son kashe su.

Ado Alero ya bayyana hakanne cikin wani rahoto binciken ƙwaƙwaf na tawagar ‘BBC Africa Eye’ wanda ake sa ran za su sake shi nan gaba a ranar Litinin.

An naɗa Ado Alero sarautar Sarkin Fulanin Ƴandoton Daji da ke jihar Zamfara a makon jiya, naɗin da ya bar baya da kura.

Naɗa Ƙasurgumin Ɗan Fashi Sarauta A Zamfara Ya Jawo An Dakatar Da Sarkin Da Ya Yi Naɗin.

Daga Yanzu Duk Wani Ɗan Zamfara Zai Iya Mallakar Bindiga Domin Ya Kare Kansa.

Rundunar yan sanda a jihar Katsina ta kubutar da Jaki da akayi garkuwa dashi.

Tini dai gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da Sarkin ‘Yandoton Daji da ke yankin karamar hukumar Tsafe ta jihar, sakamakon naɗin da ya yi.

Ana zargin Ado Alero ne ya jagoranci tawagar yaransa suka kai harin da ya yi sanadiyyar kashe gwamman mutane  da kone gidaje da shaguna a kauyen Kadisau na karamar hukumar Faskari jihar Katsina a shekarar 2019, wanda kuma aka sa kyautar miliyan biyar ga duk wanda ya kai Alero ga jami’an tsaro ko kuma ya kai labarin inda yake.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *