June 27, 2022

Najeriya: Korona Ta Kashe Mutum 8 Ta Kuma Kama 301.

Page Visited: 307
0 0
Read Time:54 Second

Daga: Suleman Ibrahim Moddibo

Sabbin alƙaluman da hukumar da ke yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta fitar a jiya Lahadi 16 ga watan Junairun shekarar 2022 sun ce, sabbin mutum 301 ne suka ƙara kamuwa da cutar Korona a ƙasar.

Jihohin da waɗanda suka kamun suka fito sun haɗa da jihar Lagos mai mutum 175 wanda ita ce kan gaba, sai mai biye mata jihar Ondo da mutum 42 jihar Osun na da 23 jihar Rivers mutam 21.

Sauran sune jihar Nasarawa mutum 16 sai Oyo inda mutum 8 suka kamu jihar Gombe 7 Kaduna 7 babban birnin tarayyar Najeriya Abuja na da mutum 1 jihar Kano 1.

Sanarwar da NCDC ta wallafa a shafin ta na Twitter ta yi nuni da cewa mutum 8 ne suka rasa rayukansu ranar inda zuwa yanzu aka sallami 224,052 da suka warke daga cutar.

Mutane 250,929 hukamar ta tabbatar da sun kamu da cutar a Najeriya yayin da mutum 3,103 suka mutu sanadiyar cutar.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *